Gwamnatin Zamfara ta Bude Makarantu 45 Cikin 75 da ta Garkame Bara

Gwamnatin Zamfara ta Bude Makarantu 45 Cikin 75 da ta Garkame Bara

  • Gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da sake bude makarantu 45 daga cikin 75 da ta garkame a shekarar da ta gabata
  • Sakataren ma’aikatar ilimin jihar, Alhaji Kabiru Attahiru ya sanar da hakan a ranar Laraba yayin da ya karba wasu baki a ma’aikatar
  • Ya bayyana cewa, kalubalen tsaro ya yi kasa a jihar shiyasa aka bude makarantun amma sauran 30 din an bar su a rufe ne har sai an ga abinda hali yayi

Gusau, Zamfara - Gwamnatin jihar Zamfara ta sake bude wasu makarantu 45 daga cikin 75 da ta rufe saboda rashin tsaro, ma’aikatar ilimi ta bayyana hakan a ranar Laraba a Gusau.

Taswirar Zamfara
Gwamnatin Zamfara ta Bude Makarantu 45 Cikin 75 da ta Garkame Bara. Hoto daga Punchng.com
Asali: UGC

Jaridar Punch ta rahoto cewa, sakataren ma’aikatar, Alhaji Kabiru Attahiru ya bayyana hakan yayin karbar bakuntar wasu mambobin kungiyar fasaha ta ilimi wadanda suka kai masa ziyara ma’aikatar.

Kara karanta wannan

Jami’an Hisbah Sun Kama Mata Masu Yawan Gaske Saboda Kwankwadar Barasa Da Karuwanci A Wata Jihar Arewa

Gwamnatin jihar ta Umarci rufe makarantun a watan Satumban 2021 bayan an sace daliban Makarantar gwamnati ta jeka ka dawo dake Kaya a karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara.

“A yayin bude makarantun, mun rarrabe su zuwa kashi uku, Koraye, dorawa da ja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Koraye sune na yankunan da babu wani kalubalen tsaro, dorawa sune makarantun da ke inda akwai kalubalen tsaro amma kadan, sai jajaye sune a yankunan dake da manyan kalubalen tsaro.”

- Attahiru yayi bayani.

Yace dukkan makarantun 75 sun fada kashin ja a lokacin da aka rufe su kuma hatsarin ne yasa aka cigaba da barinsu a rufe.

“A yau ina farin cikin sanar muku cewa sakamakon cigaban da aka samu a fannin tsaro a jihar, mun sake bude wasu makarantu 45 daga cikin 75 yayin da sauran 30 din zasu kasance a rufe.

Kara karanta wannan

Dakarun Sojin Najeriya sun Kama Wiwi ta N4m wacce Za a Kai wa ‘Yan Ta’adda a Yobe

“Gwamnati da hukumomin tsaro suna aiki tare domin tabbatar da wanzuwar tsaro a jihar.”

- Ya kara da cewa.

Gwamnatin Jigawa Ta Rufe Makarantu Yayin da Dalibai Ke Rubuta Jarabawa Saboda Fargabar Kai Hari

A wani labari na daban, gwamnatin jihar Jigawa ta ba da umarnin rufe dukkan makarantun gwamnati da ke jihar nan take bisa fargabar hare-haren da ake kaiwa makarantu a fadin jihar.

An rufe makarantun ne ba zato ba tsammani a ranar Laraba 17 ga watan Agusta yayin da daliban ke gudanar da jarrabawar kammala karatunsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel