Emeka Ihedioha
Mun kawo jerin wasu badakalolin da sabon Gwamnan Jihar Imo da kotu ta nada ya taba shiga a tarihi. Hope Uzodinma dai ba bakon EFCC ba ne.
Zuwa yanzu dai jami’an tsaro sun garkame dukkanin kofofin da suke shigar da jama’a zuwa fadar gwamnatin jahar Imo tun bayan samun labarin hukuncin da kotun koli ta yanke na tsige gwamnan jahar, Emeka Ihedioha.
An jima Kotun koli za ta yanke hukunci a karar zaben Sokoto, Imo da Kano. Shari’an karar Gwamnoni 3 za ayi a yau wanda kowa ya ke sa rai.
An binciko hannun tsohon Gwamnan jihar Imo na APC, Rochas Okorocha, cikin badakala. Wani kwamiti ya ce Rochas Okorocha ya yi sama-da-fadi da N6b a Jihar Imo.
Mun ji cewa an hurowa karamin Ministan ilmi wuta a APC kan zargin hada-kai da PDP a zaben Imo. PDP dai ta ce a shirya ta ke ta karbe sa a jihar.
Ejike Mbaka ya gano Jihar Imo za ta koma hannun ‘Dan takarar ‘Jam’iyyar APC a 2020.. Limamin Kiristan ya ja-kunnen duk wanda ba su ji dadin sakon ba, su yi tsit.
Kaakakin gwamnan jahar, Chibuike Onyeukwu ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar inda yace kungiyar mai suna ‘South East Youth Leaders’ ba ta da hurumin yin magana da yawun al’ummar jahar ko gwamnatin jahar.
Gwamna Ihedioha ya fito ya fadawa Duniya cewa akwai masu yaudarar mutane da sunan sa. Gwamnan ya ce an samu wasu bata-gari na rabawa mutane aikin karya da sunan sa a Jihar Imo
Babbar Jam’iyyar hamayya a Najeriya ta PDP ta samu gagarumar nasara a gaban kotu jiya. A Ribas Clifford Edanuko ya janye kara, eannan ya sa kotu ta tabbatar da Wike a matsayin wanda ya yi nasara.