Kotun koli za ta yanke hukunci a kan karar zaben Sokoto, Imo da Kano

Kotun koli za ta yanke hukunci a kan karar zaben Sokoto, Imo da Kano

Mu na da labari cewa an jima kadan ake sa ran cewa Alkalan kotun koli za su saurari karar wasu zabubbaka da aka yi na gwamna a 2019.

Kotun koli za ta zauna a Yau Litinin, 13 ga Watan Junairun 2020 ne domin yanke hukunci game da shari’a zaben da aka yi a irinsu jihar Kano.

Haka zalika babban kotun kasar za ta yanke hukuncin karshe a game da korafin da ake yi game da zaben gwamna da aka yi a Sokoto da Imo.

A jihar Kano, idan ba ku manta ba, Abba Kabir Yusuf na PDP ya na kalubalantar zaben da ya ba APC da kuma Abdullahi Umar Ganduje nasara.

‘Dan takarar APC a zaben gwamnan Sokoto, Ahmed Aliyu, ya shigar da kara gaban koli game da nasarar da hukumar INEC ta ba PDP a zaben bara.

KU KARANTA: Za a san Jam'yyar da za ta rike Jihar Kano zuwa 2023

Injiniya Abba Kabiru Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida ya na kalubalantar sake gudanar da wani danyen zabe da aka yi a jihar Kano.

A jihar Sokoto inda abin ya zo gaf-da-gaf, gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya lashe zabe ne da kuri’a 512, 002 a kan APC da ta samu 511, 661.

Gwamnan Imo Emeka Ihedioha zai saurari hukuncin shari’arsa da Hope Uzodimma, Uche Nowsu da Ifeanyi Ararume wanda su ka yi takara da shi.

Kotun da ke sauraron korafin zabe da na kotun daukaka kara ba su ba jam’iyyun hamayya nasara a jihohin nan a duk shari’o'in da aka yi ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel