Babu wanda ya isa ya kori makiyaya daga jahar Imo – Gwamna Emeka

Babu wanda ya isa ya kori makiyaya daga jahar Imo – Gwamna Emeka

Gwamnatin jahar Imo a karkashin jagorancin Gwamna Emeka Ihedioha ta bayyana cewa babu wanda ya isa ya sallami Fulani makiyaya daga jahar, don haka ya yi kira ga jama’a da suyi watsi da kashedin da wata kungiyar matasan ibo suka yi ga makiyaya dasu fice daga jahar cikin sa’o’i 24.

Kaakakin gwamnan jahar, Chibuike Onyeukwu ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar inda yace kungiyar mai suna ‘South East Youth Leaders’ ba ta da hurumin yin magana da yawun al’ummar jahar ko gwamnatin jahar.

KU KARANTA: Adam Zango ya ciri tuta a matsayin jarumin da ya fi taimaka ma talakawa

Gwamnan yace wannan kashedi da kungiyar ta baiwa Fulani makiyaya abin kunya ne a gareta, don haka ya nemi jama’a su yi watsi da ita. Sai dai ya kara da cewa matasan sun bada kashedin ne biyo bayan korafi da jami’an gwamnatin tarayya na kimiyya da fasaha na Owerri ta yin a cewa makiyaya sun lalata musu gonakansu.

“Gwamnatin jahar Imo ta nesanta kanta da wa’adin awanni 24 da wata kungiya ta baiwa Fulani makiyaya su fice daga jahar Imo saboda wai sun ji jami’ar kimiyya dake Owerri ta yi zargin makiyaya sun lalata mata gonarta.

“Gwamnatin Imo a karkashin Gwamna Emeka Ihedioha ta ji kunya game da wannan kashedi, don haka ta dauki dukkanin matakin daya kamata domin kare aukuwar rikici, karya doka da oda da kuma tashin tashina a jahar.” Inji shi.

Daga karshe gwamnan ya kara da yin kira ga jama’a dasu zauna lafiya da juna ba tare da tsangwama ba, saboda a cewarsa jahar Imo jahace dake cikin aminci da zaman lafiya, kuma tana da kyakkyawar alaka da makwabtanta da bakin dake kwarara zuwa cikinta.

A wani labarin kuma, gwamnan jahar Yobe, Mai Mala Buni ya sanya kyautar N100,000 ga duk mutumin da yayi rajista da gwamnati, ya karbi irin bishiya, ya dasa bishiyar sa’annan ya yi dawainiya da ita tsawon shekara 1 cur!

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da yake kaddamar da rabon irin bishiyoyi a garin Damaturu, babban birnin jahar Yobe, inda yace ya kirkiro wannan tsari ne domin yaki da kwararowar hamada.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel