Hukuncin kotun koli: Buba Galadima ya yi hasashen abunda ka iya zama makomar Ganduje
Tsohon jigon jam’iyyar Congress for Progressive Change (CPC) kuma tsohon aminin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Buba Galadima, a jiya Laraba, 15 ga watan Janairu ya bayyana hukuncin kotun koli wacce ta kaddamar da Hope Uzodinma zababben gwamnan jihar Imo a matsayin babban almara a tarihin duniya.
Ya ce: “Abunda ya faru shine cewa kotun koli a yanzu ta daure kanta saboda ta yaya Za su yiwa Emeka Ihedioha haka sannan su ki yiwa Abba Kabiru Yusuf a Kano? Iri abu guda sak ne ya faru a Kano.
“Idan har ya zama dole a soke zabe, ya kamata ya kasance a matakin rumfar zabe ya kamata a soke a cewar kotun koli. Amma a Kai, ba a soke kuri’un a wajen zabe ba; ba a soke su a matakin unguwa ba sai dai an soke sune a matakin karamar hukuna. Don haka idan har ba a ce Ganduje ya tafi ba sannan aka fadi wani abu sabanin haka, lallai Najeriya za ta ga tashin hankalin.”
Hukumar zabe mai zaman kanta a halin da ake ciki, ta gabatar da takardar shaidar cin zabe ya Uzodinma a jiya Laraba.
KU KARANTA KUMA: Gwamnan Borno ya yi umurnin dakatar da likita kan karkatar da magungunan asibiti
Kwamishinan zabe na kasa da ke kula d Rivers, Bayelsa da Edo, May Agbamuche-Mba be ya gabatar da takardar a lokacin wani kwarya-kwaryan biki da aka shirya a hedkwatar hukumar da ke Abuja.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng