Hope Uzodinma ya yi karin haske game da binciken Okorocha da Ihedioaha

Hope Uzodinma ya yi karin haske game da binciken Okorocha da Ihedioaha

A game da umarnin da ya bada na samun rahoto da lissafin kashe kudin gwamnatocin da aka yi a baya, sabon gwamman jihar Imo, ya yi wa jama’an jiharsa karin-haske.

Kamar yadda mu ka samu labari, Hope Uzodinma ya bayyana cewa bai taba cewa zai binciki gwamnatin baya ta da shude ta tsohon gwamna Rochas O. Okorocha ba.

Sabon gwamnan ya yi wannan jawabi ne a cikin karshen makon da ya wuce, bayan ya zagaya ya duba wasu gine-gine da ke cikin gidan gwamnatin jihar da ke Garin Owerri.

Uzodinma ya ce ko da cewa aikin shugabanci ya kunshi bincike da bin kwa-kwaf, umarnin da ya ba babban Akanta na jihar na kawo masa rahoto ya samu mummunan fassara.

“Lokacin da na bukaci a kawo mani rahoton halin da duka ma’aikatu su ke ciki, wasu sun yi mani wata fassata dabam ko su ka dauka ina neman bayani ne domin in ye bincike.”

KU KARANTA: Imo: Kungiya ta sa alamar tambaya game da nasarar APC a kotun koli

“Ban taba cewa zan binciki wani ba. Shugabanci ya hada da bincike idan ta kama; saboda ina bukatar samun bayani ne saboda babu wani zama da aka yi na mika mulki.”

“Idan wajen bincike da bin diddiki mun ga cewa akwai bukatar a kira wani ya amsa tambayoyi, sai ayi hakan, gwamnati ba za ta gushe da yin wannan ba.” Inji Uzodinma.

“Aiki na shi ne in jagoranci jama’a, idan a kan hanya na ga akwai bukatar a binciki wani lamari, zan yi hakan, amma ka da wanda ya ari baki na ya ci mani albasa, don ba ce ba.”

A game da halin da ya samu gine-ginen da ke cikin gidan gwamnati, Mai girma Hope Uzodinma, ya bayyana cewa za a fara gyare-gyare kwanan nan domin a soma aiki a jihar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng