EFCC, SPIP sun taba cafke sabon Gwamnan Jihar Imo Hope Uzodinma

EFCC, SPIP sun taba cafke sabon Gwamnan Jihar Imo Hope Uzodinma

An taba jifan Hope Uzodinma da zargin cewa bai kammala makarantar sakandare a 1982 ba. Sau da yawa kuma ana kai kararsa gaban kotu da hukumomin EFCC da SPIP.

Sanata Hope Uzodinma shi ne wanda ake sa ran za a rantsar a matsayin gwamnan Imo an jima.

1. SPIP

Hukumar SPIP da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa domin karbo kadarorin gwamnati a hannun jama’a ta taba kama Hope Uzodinma bisa zargin handame Dala miliyan $12 na wata kwangilar yasa. Okoi Obono-Obla ya ce NPA ce ta bada wannan kwangila da aka cinye kudinta.

2. Oputa

A wani bincike da aka taba yi a karkashin Alkali Chukwudifu Oputa a 2001, an zargi Hope Uzodinma da laifin tura wasu kudi na hukumar NIMSA zuwa asusun wani tsohon Shugaban kasa. Ana kuma zargin cewa an ba shi kwangilolin bogi kafin EFCC ta sa shi ya maido kudin.

KU KARANTA: Abubuwan da ya kamata ku sani game da sabon Gwamnan Imo

3. EFCC

A farkon 2009 ne jami’an hukumar EFCC su ka cafke Hope Uzodinma bayan wasu Bayin Allah da su ka fito daga yankinsa sun shigar da kara a kansa. Mutanen Orlu sun ce wani Bankin Najeriya ya taba zargin ‘Dan takarar Sanatansu da laifin wawura da handamar wasu makudin kudi.

4. WAEC

A 2013 ne fitaccen Lauya Festus Keyamo ya kai karar hukumar WAEC a gaban kotu, ya na mai zargin cewa Hope Uzodinma bai da ainihin takardun jarrabawa. A dalilin wannan ya sa Keyamo wanda ya zama Ministan yanzu ya bukaci a tursasawa WAEC ta fito da takardun Sanatan.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng