Wata sabuwa: An garkame fadar gwamnatin jahar Imo bayan hukuncin kotun koli daya tsige gwamnan
Zuwa yanzu dai jami’an tsaro sun garkame dukkanin kofofin da suke shigar da jama’a zuwa fadar gwamnatin jahar Imo tun bayan samun labarin hukuncin da kotun koli ta yanke na tsige gwamnan jahar, Emeka Ihedioha.
Jaridar Punch ta ruwaito jami’an tsaro sun bayyana cewar an basu umarnin su hana duk wani shige da fice zuwa ciki da wajen fadar gwamnatin, kamar yadda suka tabbatar ma wakilinta.
KU KARANTA: Gwamnatin tarayya ta bayyana rundunar ‘matasan tsaro na yarbawa’ a matsayin haramtacciya
Idan za’a tuna da yammacin Talata, 14 ga watan Janairu ne Alkalan kotun koli suka tabbatar da haramcin nasarar da Gwamna Ihedioha ya samu a zaben 2019, don haka ta tsige shi, sa’annan ta tabbatar sanar da Sanata Hope Uzodinma a matsayin halastaccen zababben gwamnan jahar.
Majalisar Alkalan kotun koli guda bakwai a karkashin jagorancin babban Alkalin Alkalai, Mai sharia Tanko Muhammad ne suka zartar da hukuncin, inda suka ce Sanata Hope ya lashe zaben ranar 9 ga watan Maris.
A wani labari kuma, sabon gwamna Hope Uzodinma, ya ce kotu ta dawo masa da hakkinsa. Uzodinma, wanda yayi magana ta bakin mai magana da yawunsa, Declan Emelumba, ya ce tun kafin rana irin ta yau ya kasance mai imani da Alkalan Najeriya.
Yace: "A yau, kotu mafi girma a kasar nan ta dawo mini da hakkin na da al'ummar jihar Imo suka bani. Hakan na nufin cewa nasarar da al'ummar jihar Imo suka bani, amma aka kwace min, ya daow. Ina mmai godiya ga Allah madaukaki,"
Emelumba ya ce sabon gwamnan zai koma jihar Imo gobe kuma zai yi jawabi ga al'ummar jihar.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng