2020: Fasto Mbaka ya fadawa Mabiyansa Jam’iyyar APC za ta dawo Imo
Shugaban babban cocin nan na Adoration Ministry da ke jihar Enugu, Ejike Mbaka, ya ce Sanata Hope Uzodinma zai karbe mulkin jihar Imo.
A sakonsa na sabuwar shekara, Rabaren Ejike Mbaka ya bayyana cewa Jihar Imo za ta koma hannun ‘Dan takarar APC, Hope Uzodinma.
A zaben da aka yi a 2019, Rt, Hon. Emeka Iheidoha na PDP ne ya lashe zabe a jihar Imo, amma kuma Limamin ya ce APC za ta mulki jihar.
Rabaren Mbaka bai bayyanawa jama’a yadda wannan lamari zai auku ba, amma dai ya tabbatar da cewa ya hango APC ta na mulkin jihar Imo.
Limamin ya ja-kunnen wadanda ba za su ji dadin sakon na sa ba da cewa ka da su huce fushinsu a kansa, domin za su gamu da fushin Ubangiji.
Jama’a da dama ne su ka halarci zaman cocin da aka yi inda aka yi wa kasa addu’o’i, sannan Faston ya bayyana abubuwan da za ayi a 2020.
KU KARANTA: Ayo Fayose ya fara sabuwar shekarar 2020 da jan kunnen Magauta
Karamin Ministan harkokin ma’danai a Najeriya, Dr. Uche Ogar ya na cikin wadanda aka yi zaman cocin sabuwar shekarar da su a Garin Enugu.
“Abubuwa da yawa za su faru a Najeriya a shekarar nan ta 2020 wanda za su ba Maza da Mata mamaki. Amma komai ya na hannun Ubangiji.”
“Duk da abubuwan da za su faru akwai alamun nasara a 2020. A jihar Imo akwai nasara.”
“Mutanen Imo sun sha wahala, amma Ubangiji zai turio masu wanda zai kawo masu sauki. Wani zai zo da sabuwar tuta ya dawo da martabar kasar.”
“Za a samu sabon shugabanci da zai ratsa jihar Imo.”
“Al’ummar Imo za su yi farin ciki. Na tofawa Hope Uzodinma albarka; kuma na ba sa tabarrukin karbar mulki.”
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng