Emeka Ihedioha da Nyesom Wike sun yi nasara a Kotun karar zaben 2019

Emeka Ihedioha da Nyesom Wike sun yi nasara a Kotun karar zaben 2019

Jam’iyyar hamayya ta PDP ta samu gagarumar nasara a gaban kotu a wannan makon bayan da a ka ba gwamnan Imo, Emeka Ihedioha da Takwaransa na Ribas, Nyesom Wike, gaskiya a wasu shari’a da a ke yi.

A Ranar Talata 30 ga Watan Yuli, 2019, Kotun kolin kasar nan ta yi watsi da karar da Sanata Samuel Anyawu ya shigar ya na mai kalubalantar yadda Emeka Ihedioha ya zama gwamnan jihar Imo a zaben bana.

Alkali mai shari’a John Okoro, wanda ya duba wannan kara, ya yi watsi da rokon da Samuel Anyawu ya kawo gaban kuliya. Alkalin ya bayyana cewa mai karar ya gaza gamsar da babban kotu da tarin hujjoji.

KU KARANTA: Wasu Sanatocin PDP sun samu rikon kujerun kwamiti a Majalisa

Sai dai ma a ka nemi mai karar ya biya kudi N200,000 ga wadanda ya ke tuhumar a kotu. Anyawu ya na kukan cewa ba Emeka Ihedioha ba ne ainihin wanda ya lashe zaben fitar da gwani da PDP ta shirya a jihar Imo.

A jihar Ribas kuma, kotun da ke sauraron karar zaben 2019, ya yi fatali da karar gwamna mai-ci, Nyesom Wike na PDP. Alkalan kotun sun bayyana cewa babu shakka PDP ce ta lashe zaben 2019 bayan an janye kara.

‘Dan takarar jam’iyyar adawa ta PPP a zaben gwamnan Ribas na bana, Clifford Edanuko da jam’iyyarsa sun janye karar da su ka shigar kwanaki. Wannan ya sa aka tabbatar da nasarar jam’iyyar a babban zaben.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel