Imo: Korarren gwamna PDP ya yi magana a kan hukuncin kotun koli a karo na farko

Imo: Korarren gwamna PDP ya yi magana a kan hukuncin kotun koli a karo na farko

A ranar Laraba ne gwamnan jihar Imo da kotun koli ta kwace kujerarsa, Emeka Ihedioha, ya bayyana cewa bai amince da hukuncin da kotun koli ta zartar a kansa ba.

A wani jawabi mai dauke da sa hannunsa, Ihedioha ya bayyana cewa tsigewar da kotun kolin ta yi masa ya saba da zabin mutanen jihar Imo.

Amma duk da hakan, Ihedioha ya bayyana cewa ya karbi hukuncin da kotun ta zartar na tsige shi kuma tuni ya saka maganar mika ga mulki ga sabon gwamna mai jiran gado, Sanata Hope Uzodinma, a gaba.

Ya kara da cewa ya kawo gayre-gyare masu yawa a harkar gudanar da gwamnati a jihar Imo a cikin dan kankanin lokacin da ya shafe yana mulkin jihar.

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa tuni ya umarci dukkan hadimansa su mika kadarori da duk wasu kaya mallakar gwamnati ga sabuwar gwamnatin da zata fara mulki, tare da bayyana cewa ba zai lamunci lalata kadara ko kudin gwamnati ba.

Imo: Korarren gwamna PDP ya yi magana a kan hukuncin kotun koli a karo na farko
Emeka Ihedioha
Asali: UGC

A ranar Talata ne kotun koli ta kwace kujerar gwamnan Imo, Emeka Ihedioha, dan jam'iyyar PDP tare da tabbatar da Hope Uzodinma, dan jam'iyyar APC a matsayin halastaccen zababben gwamnan jihar.

DUBA WANNAN: Atiku ya bawa Ihedioha muhimmiyar shawara bayan kotu ta karbe kujerarsa ta bawa APC

Kotun, mai alkalai bakwai a karkashin jagorancin alkalin alkakalai na kasa (CJN), Mohammed Tanko, ta ce ba Ihedioha ne halastaccen zababben gwamnan jihar Imo ba.

Tuni hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bawa Sanata Hope Uzodinma na jam'iyyar APC shaidar samun nasarar lashe zaben kujerar gwamnan jihar Imo.

INEC ta bashi takardar shahadar ne ranar Laraba, kasa da sa'o'i 24 bayan kotun koli ta soke zaben Emeka Ihedioha a matsayin gwamnan jihar Imo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel