ISOPADEC: Kwamiti ya zargi Okorocha da yin sama-da-fadi da N6b a Jihar Imo

ISOPADEC: Kwamiti ya zargi Okorocha da yin sama-da-fadi da N6b a Jihar Imo

Kwamitin da gwamnan jihar Imo, Rt. Hon. Emeka Ihedioha, ya kafa domin binciken hukumar ISOPADEC ya gano irin barnar da gwamnatin baya ta yi.

Gwamnan jihar ya bukaci ayi masa bincike a game da ayyukan da ISOPADEC mai kula da yankunan da ke da arzikin mai ta yi tsakanin 2011 zuwa 2019.

Wannan bincike ya nuna cewa akwai hannun tsohon gwamnan Imo Rochas Okorocha wajen batar da kudi N6, 044, 774, 341. 37 da aka warewa hukumar jihar.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto yau cewa binciken ya zargi tsohon gwamnatin jam’iyyar APC da bi ta kan tulin kudin da ke cikin asusun hukumar ISOPADEC.

KU KARANTA:

ISOPADEC: Kwamiti ya zargi Okorocha da yin sama-da-fadi da N6b a Jihar Imo
Emeka Ihedioha ya na binciken gwamnatin Rochas Okorocha
Asali: UGC

Bayan haka, kwamitin ya zargi gwamnatin Okorocha da kashe wasu daga cikin kudin wannan hukuma wajen sayen motoci da na’urar bada wutan lantarki.

Binciken da aka yi, ya nuna cewa an yi amfani da wadannan motoci da gwamnati ta saya wajen yakin neman zabe da hannun Chike Okafor da Paschal Obi.

Ana kuma zargin Rochas Okorocha wanda ya zama Sanata a yanzu da karkatar da Naira biliyan 311 da gwamnatin tarayya ta ba jihar domin biyan albashi.

Wannan kwamiti ta ce Okorocha ya kuma wawuri kudin al’umma daga hukumar da ke kula da makarantun sakandare, sannan an saci fanshon ma’aikata.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel