Mace ta gari: Matar tsohon gwamnan jahar Imo ta kwantar masa da hankali a idon Duniya

Mace ta gari: Matar tsohon gwamnan jahar Imo ta kwantar masa da hankali a idon Duniya

Masu iya magana suna cewa “Mace ta gari ita ce sila ta zama lafiya” hakan ya tabbatar a bahallatsar siyasar jahar Imo, inda uwargidar korarren gwamnan jahar Imo, Emeka Ihedioha, Ebere Ihedioha ta kwantar masa da hankali tare da rarrashinsa.

Da yammacin Talata, 14 ga watan Janairu ne Alkalan kotun koli suka tabbatar da haramcin nasarar da Gwamna Ihedioha ya samu a zaben 2019, don haka ta tsige shi, sa’annan ta tabbatar sanar da Sanata Hope Uzodinma a matsayin halastaccen zababben gwamnan jahar.

KU KARANTA: Duniya ina za ki da mu? Matashi ya lakada ma mahaifiyarsa dan banzan duka a jahar Ebonyi

Mace ta gari: Matar tsohon gwamnan jahar Imo ta kwantar masa da hankali a idon Duniya
Emeka da Ebere
Asali: Facebook

Majalisar Alkalan kotun koli guda bakwai a karkashin jagorancin babban Alkalin Alkalai, Mai sharia Tanko Muhammad ne suka zartar da hukuncin, inda suka ce Sanata Hope ya lashe zaben ranar 9 ga watan Maris.

Sai dai uwargida Ebere ba ta nuna gazawa wajen rarrashin mijinta ba, wanda hotunansa suka dinga yawo a kafafen sadarwar zamani yayin da yake zubar da hawaye bayan samun labarin hukuncin kotun kolin da ta yi awon gaba da shi.

Ebere ta wallafa wani hotonta da gwamnan a shafin ta na kafar sadarwar zamani na Twitter inda ta yi masa taken “Ya masoyi na, ya miji na, ya abokina, Maigida na! Ina tare da kai.” Ebere da Emeka suna da yara hudu a tsakaninsu.

A wani labarin kuma, hukumar zabe mai zaman kanta na INEC ta mika ma Sanata Hope Uzodinma takardar shaidar lashe zaben gwamnan jahar Imo a ranar Laraba, 15 ga watan Janairu, wanda hakan ke nufin ta tabbata shi ne halastaccen gwamnan jahar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel