Gwamna Hope Uzodinma ya yi sabbin nade nade guda 4 masu muhimmanci

Gwamna Hope Uzodinma ya yi sabbin nade nade guda 4 masu muhimmanci

Gwamnan jahar Imo, Sanata Hope Uzodinma a ranar juma’a, 17 ga watan Janairu ya zabo wasu mutanensa na hannun dama inda ya nada muhimman mukamai a jaririyar gwamnatinsa.

Daily Trust ta ruwaito sabbin nade naden sun hada da nadin Nnamdi Anyaehie a matsayin shugaban ma’aikatan gidan gwamnati, Oguike Nwachukwu a matsayin mashawarci a kan harkokin watsa labaru.

KU KARANTA: Kara da kiyashi: Yadda wani mutumi ya kashe abokinsa har ya cinye marainansa

Sauran sun hada da nadin Comas Iwu a matsayin sakataren gwamnatin jahar Imo, da kuma C.O.C Akaolisa a matsayin babban lauyan gwamnati kuma kwamishinan shari’a a jahar Imo.

Daga karshe majiyar Legit.ng ta ruwaito gwamnan ya bayyana cewa nadin ya fara aiki ne nan take.

Da yammacin Talata, 14 ga watan Janairu ne Alkalan kotun koli suka tabbatar da haramcin nasarar da Gwamna Ihedioha ya samu a zaben 2019, don haka ta tsige shi, sa’annan ta tabbatar sanar da Sanata Hope Uzodinma a matsayin halastaccen zababben gwamnan jahar.

Majalisar Alkalan kotun koli guda bakwai a karkashin jagorancin babban Alkalin Alkalai, Mai sharia Tanko Muhammad ne suka zartar da hukuncin, inda suka ce Sanata Hope ya lashe zaben ranar 9 ga watan Maris.

A wani labarin kuma, dattijon Arewa, Alhaji Tanko Yakasai ya bayyana cewa akwai yiwuwar jama’an kabilar Ibo su samu mulkin Najeriya amma fa sai sun kulla kyakkyawar alaka da sauran yankunan kasar, musamman Arewa.

Yakasai ya bayyana haka ne cikin wata hira da yayi da gidan talabijin na Channels a ranar Juma’a, inda yace: “Yan kabilar Ibo suna da daman samun shugaban kasa a Najeriya nan gaba kadan ko kuma a can gaba, a tsarin siyasar Najeriya ba’a samun mulki sai an hada kai da yankunan Arewa da kudu.

“Dole ne sai inyamurai sun fara kokarin samun hadin kan sauran yankunan kasar musamman ma Arewa, ba wai kawai za su tsaya su yi ta korafi bane, kamata ya yi su fara kokarin kulla alaka da jama’a domin su bayyana manufofinsu, wannan abu ne mai yiwuwa.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel