Manyan matakan da sabon Gwamnan Imo ya fara dauka bayan hawa mulki
An rantsar da Sanata Hope Uzodinam a matsayin sabon gwamnan jihar Imo a yammacin Ranar Laraba, 15 ga Watan Junairun 2020.
Ku na sane cewa an yi hakan ne bayan Alkalan kotun kolin sun ruguza nasarar Emeka Ihedioha a zaben gwamnan da aka yi a bara.
Daga hawansa gwamna zuwa yanzu, Hope Uzodinma ya dauki wasu manyan mataki biyu:
1. Garkame asusun bankin gwamnatin Imo
Jim kadan bayan kotu ta tabbatar da Hope Uzodinma a matsayin gwamnan Imo, ya bada umarni cewa ka da wani banki ya fitar da kudi daga cikin asusun gwamnati da umarnin tsohon gwamna.
Sabon gwamnan ya bada wannan sanarwa ne ta bakin Sarkin yakin neman zabensa, Cif Cosmos Iwu. An bada wannan umarni ne ga bankuna da babban Akantan gwamnatin Imo Ranar Talata.
KU KARANTA: Hope Uzodinma ya karbi ragamar mulkin Jihar Imo
2. Binciken gwamnatocin da su ka shude
A Ranar Laraba watau 15 ga Watan Junairu, 2020, sabon gwamnan Imo ya bada umarni a binciki gwamnonin baya. Hope Uzodinma ya ce zai binciki abin da ya gudana a jihar tun daga 2010.
Binciken zai shafi tsofaffin gwamnoni; Ikedi Ohakim, Rochas Okorocha da Emeka Ihedioha.
3. Dakatar da biyan kudin kwangiloli
A jawabinsa na farko bayan ya dare mulki, Hope Uzodinma ya bada umarnin dakatar da biyan duk wani kudin kwangila a jihar. Sannan gwamnan zai duba duk wasu kwangiloli da ake yi.
4. Afuwa
Sanata Hope Uzodinma ya kuma bayyana cewa ya yafewa duk wadanda su ka hada-baki wajen murde zabensa da farko. Gwamnan ya nuna cewa ya yi afuwa, sannan ya ce zai kawo gyara.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng