Zaben Shugaban kasan Najeriya
Kungiyar Arewa Consensus for Jonathan (ACJ) ta bayyana nadamar kin zaben Jonathan a 2015, tana yabawa da irin ci gaban da ya kawo yankin Arewa a fannin ilimi.
Fadar shugaban kasa ta yi martani ga Atiku Abubakar kan wasu malamai da ya yi a kan Bola Tinubu. Gwamnatin tarayya ta ce Atiku na yi wa Bola Tinubu hassada.
Yunusa Tanko, shugaban kungiyar 'Obidient' ya tabbatar da cewa Peter Obi zai iya zama shugaban kasa a 2027, yana mai cewa magudi ne ya hana Obi nasara a 2023.
Atiku Abubakar ya caccaki gwamnatin Bola Tinubu kan tsare-tsaren da ta kawo na tattalin arziki. Atiku ya ce an yi masa fashin kuri'u a zaben 2023 da ya gabata.
Tsohon hadimin shugaban kasa, Doyin Okupe ya ce Shugaba Bola Tinubu na yin abin da ya dace kuma ƴan Najeriya za su kara ba shi dama a babban zaben 2027.
Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta dauki zafi bayan tsohon dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya caccaki matakan da ta dauka kan tattalin arziki.
Minista ya umarci ‘yan sanda su sallama takardun sharia da yara masu zanga-zanga. Ministan shari’a, Lateef Fagbemi SAN zai karbi shari'ar yara masu zanga-zanga.
Kananan hukumomi sun samu ‘yanci, amma har yanzu kusan gwamnoni ne ke da ta-cewa wajen takara. Akwai rudani game da cin gashin kan da kananan hukumomin.
Peter Obi ya na cikin wadanda suka taya Yakubu Gowon murnar cika shekaru 90 a makon da ya gabata. Sai dai magana a kan Yakubu Gowon ya jawowa Obi matsala a siyasa.
Zaben Shugaban kasan Najeriya
Samu kari