Zaben Shugaban kasan Najeriya
Ministan ayyuka, Injiniya Dave Umahi ya bayyana cewa ba makawa sai shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya samu nasara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa babu wani ɗan Arewa mai hankali da zai mara wa APC baya a zaɓen 2027. Yusuf Dingyadi, ya ce ‘yan majalisar PDP sun fi na APC aiki.
Tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi ya yabi tsohon shugaban kasa, Ibrahim Badamasi Babangida bisa bayyana wanda ya ci zaben 12 ga watan Yuni, 1993.
Jagoran NNPP na ƙasa, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa yana da ƙwarin guiwar cewa jam'iyyarsa ce za ta samu nasara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Kungiyar matasan NYFA ta ce rikicin PDP ba zai hana Atiku takara a 2027 ba, ta bukaci shugabanni su hada kai don ceto jam’iyya daga barazanar wargajewa.
Jam'iyyar APC ta fara gangamin yakin neman zaɓen Gwamna Nasir Idris da Bola Ahmed Tinubu karo na biyu a 2027, ta ce sun cancanci tazarce a kan kujerunsu.
Karamin Ministan tsaro, kuma tsohon gwamnan Zamfara, Bello Matawalle ya bayyana cewa 'yan Arewa su na ganin amfanin mulkin Bola Ahmed Tinubu a fannoni da dama.
Jam'iyya mai mulki ta APC ta bayyana cewa duk da kamun kafa da ta samu labarin Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya na yi, ba ta ta bari ya dawo cikinta ba.
Shugaban bankin AfDB, Akinwumi Adesina ya musanta rahotannin da ke yawo a kafafen watsa labarai cewa yana da niyyar neman zama shugaban kasa a zaɓen 2027.
Zaben Shugaban kasan Najeriya
Samu kari