Zaben Shugaban kasan Najeriya
Gwamnonin jihohin kasar nan sun fara neman a lallaba shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a kan ya taka burki kan shirin biyan kananan hukumomi kudinsu kai tsaye.
Rahotanni daga fadar gwamnatin jihar Bauchi sun nuna cewa nan ba da jimawa da Peter Obi zai fice daga LP zuwa jam'iyyar PDP a shirye-shiryen 2027.
Jam'iyyar adawa ta PDP ta bayyana cewa maganar cewa akwai shirin sake tsayar da Goodluck Ebele Jonathan takarar shugaban kasa ba ta da tushe ballantana makama.
Rahotanni sun bayyana cewa akwai shirin da wasu 'yan siyasa ke yi na jawo tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan ya sake neman kujerar a zaben 2027 mai zuwa.
Tsohon sakataren yada labarai a PDP, Kola Ologbodinya ya bayyana fargaba a kan yiwuwar rugujewar jam'iyyarsa, wanda ya danganta da hukuncin da kotu za ta yanke masu.
Fitaccen malamin addinin Kirista a Najeriya, Fasto Chukwuemeka Cyril Ohanaemere ya bayyana kudurinsa na tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027 mai zuwa.
Daya daga cikin jagororin PDP, Kola Ologhondinyan ya bayyana cewa APC ta kwana da sanin cewa akwai gagarumin shirin da zai kawo karshen mulkinta a 2027.
Ministan harkokin jiragen sama da ci gaban sashen, Festus Keyamo, ya bayyana cewa jam'iyyar PDP ba ta da katabus a zabe mai zuwa, wanda zai sa APC ta lashe zabe.
Tsohon Mataimakin Shugaban PDP na kasa, Bode George ya bayyana cewa PDP za ta yi babban kuksure matukar ta sake tsayar da Atiku Abubakar takarar shugaban kasa.
Zaben Shugaban kasan Najeriya
Samu kari