Zaben Najeriya
A lokacin da ƴan adawa ke kokarin samar da ƙawancen da zai kifar da gwamnatin APC, INEC ta ce ta karbi buƙatun ƙungiyoyin siyasa 91 don zama jam'iyyun siyasa.
Shugaban ƙungiyar gwamnonin APC, Hope Uzodinma ya ce jam'iyyarsa na da karfin da bai kamata ƴan adawa su tsorata ta ba, ya shawarci ƴan jam'iyya kan tallata ta.
Wani rahoto ya nuna cewa ana shirin nada sabon shugaban hukumar INEC da zai zama dan amshin Shatar gwamnatin Tinubu don samun damar magudin zabe a 2027.
Majalisar wakilai ta yi karatu na biyu wa kudirin mayar da zaben gwamnoni da shugaban kasa rana 1 a Najeriya. Ana sa ran za a fara aiki da shi a 2027.
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Pat Utomi ya ce manyan ƴan siyasar ƙasar nan sun tabbatar da sha'awar aiki tare don ƙwato mulki daga hannun Bola Tinubu.
Shugaban jam'iyyar SDP na kasa, Shehu Musa Gabam ya ce sun shirya kwace mulki a hannun Bola Tinubu bayan tsofaffin Sanatoci da Ministoci sun koma SDP.
Ministan yada labarai da wayar da kan jama'a a Najeriya, Mohammed Idris ya bayyana cewa dole ce ta tilasta wa Bola Ahmed Tinubu kakaba dokar ta baci a Ribas.
Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya ce fushi da jin haushi da kuma hassada ba zai taimaka wa 'yan adawa su kayar da Bola Tinubu ba a siyasa.
Rahotanni sun ce yunkurin kafa kawancen jam’iyyun adawa domin tunkarar Bola Tinubu a 2027 na fuskantar cikas saboda takarar Atiku Abubakar da batun yanki.
Zaben Najeriya
Samu kari