Jihar Edo
Olumide Akpata ya bayyana cewa kawo yanzu ya samu bayanai marasa daɗi dangane da zaben gwamnan da ke gudana a jihar Edo, ya ce zai bincika lamarin.
Sabuwar rigima ta barke a wata rumfar zabe da ke karamar hukumar Orhionmwon ta jihar Edo a ranar Asabar bayan da jami'an INEC suka manta da takardar rubuta sakamako.
Rahotanni sun bayyana cewa jami'an hukumar EFCC sun cika hannu da wasu mutane uku da ake zargin suna sayen kuri'u a yayin da ake gudanar da zaben jihar Edo.
Kwamishinar hukumar zabe a jihar Edo, Farfesa Rhoda Gumus ta ce ko nawa aka kawo mata na cin hanci ba za ta taɓa karba ba domin kare mutuncinta da take da shi.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana cewa za ta dora sakamakon zaben gwamnan jihar Edo a kan na'urar IReV idan babu matsalar sabis.
Dan takarar jam'iyyar APC a zaben gwamnan jihar Edo da yanzu haka ke gudana, Monday Okpebholo ya kada kuri'arsa a rumfar zabe mai lamba 001, gundumar Uwessan, Esan.
Wani jigo a jam'iyyar APC mai adawa a jihar Edo, Francis Okoye, ya yi hasashen cewa dan takarar APC, Monday Okpebholo ne zai lashe zaben gwamnan jihar.
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta bukaci mutanen jihar Edo da su koma gidajensu bayan sun fito sun kada kuri'unsu a zaben gwamnan jihar na ranar Asabar.
Jigo a PDP, Dare Glintstone Akinniyi ya yi hasashen cewa Asue Ighodalo zai doke Monday Okpebolo na APC da kashi 75 cikin 100 na kuri'un da za a kada a zaben Edo.
Jihar Edo
Samu kari