Jihar Edo
Hukumar zabe ta INEC ta yi magana kan fara fitar da sakamakon zabe inda musanta fara sanar da yadda aka gudanar da zaben a yau Asabar a jihar Edo.
A yau mutane na zaben sabon gwamnan jihar Edo. Gungun kungiyoyi na Nigeria Civil Society Situation Room (NCSSR) sun ce an saye kuri’un talakawa a zaben da burodi.
Mataimakin Sufeto-Janar na 'yan sandan Najeriya, Frank Mba, ya bayyana cewa masu kada kuri'a sun fito sosai domin gudanar da zaben gwamnan jihar Edo.
Zaben gwamna naa daya daga cikin zabubbukan da ake gudanarwa a Najeruya domin zabar shugabanni. Akwai hanyoyin da ake bi wajen samun wanda ya yi nasara.
Sakamakon zaben gwamnan jihar Edo da ke gudana yau sun fara shigowa daga rumfunan zabe daban-daban. Kasance da Legit Hausa domin ganin sakamakon kai tsaye.
Yiaga Africa ta zargi wakilan jam'iyyar PDP da APC da ba masu kada kuri'a toshiyar N10,000 domin su zabi 'yan takararsu a zaben gwamnan jihar Edo da ke gudana.
Dan takarar jam'iyyar PDP a zaben gwamnan jihar Edo, Asue Ighodalo, ya bayyana cewa shi ne wanda zai samu nasara a zaben na ranar Asabar, 21 ga watan Satumba.
Hukumar zabe ta INEC a jihar Edo ta tsawaita lokutan gudanar da zabe inda ta ba da dalilai na ruwan sama da kuma rashin kawo kayan zaben a kan lokaci.
Tsohon gwamnan jihar Edo, Sanata Adams Oshiomole, ya musanta zargin cewa jam'iyyar APC ta tanadi kudi domin siyan kuri'u a hannun a zaben gwamnan jihar.
Jihar Edo
Samu kari