Zaben Edo
Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya mika godiyarsa ga Nyesom Wike a kan rawar da ya taka yayin zaben gwamnan jihar da ya gabata a ranar Asabar har ya lashe.
Dan takarar gwamna a karkashin jam'iyyar APC a zaben jihar Edo da ya gabata, Fasto Ize-Iyamu, ya yi kira ga Gwamna Godwin Obaseki da ya dawo jam'iyyar APC.
Adams Oshiomhole ya yi magana, ya ce duk da APC ta rasa jihar Edo, da sauransa tukuna. Tsohon Gwmnan bai yi magana kan masu ganin laifinsa a rashin nasarar ba.
Peters Osawaru Omiragbon, dan takarar jam’iyyar National Conscience Party (NCP) a zaben gwamnan Edo da aka kammala, ya nemi a soke zaben saboda cire sunansa.
Jam’iyyar All Progress Congress (APC) reshen Edo ta yi watsi da rade-radin da ke yawo na cewa ta fatattaki Adams Oshiomhole, tsohon shugaban jam'iyyar na kasa.
Shugabar kotun daukaka kara, Justis Monica Dongban-Menem ta kafa kotun sauraron karar zabe domin duba korafe korafe da zai fito daga zaben gwamnan jihar Edo.
Zababben gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya jaddada cewa ba zai bar jam’iyyar PDP wacce ta bashi damar lashe zabe ba zuwa ta APC wacce ta hana shi takara.
Gwamna Godwin Obaseki ya yi jinjina ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari kan zaben gwamnan Edo, ya bayyana cewa ya yi nasarar lashe zaben ne saboda adalcinsa.
Jiya Rabiu Kwankwaso ya yi magana bayan Jam’iyyar PDP ta lashe zaben Jihar Edo. Tsohon Gwamnan ya ce barazanar wasu kasashen waje sun taimaka wajen nasarar PDP.
Zaben Edo
Samu kari