Bar murna karenka ya kama kura: Ƙusan APC ya ƙalubalanci nasarar Obaseki

Bar murna karenka ya kama kura: Ƙusan APC ya ƙalubalanci nasarar Obaseki

- Ahmed Suleiman Wambai, wani jigon APC ya bayyana cewa jam’iyyarsa na iya kalubalantar nasarar Obaseki a kotu

- Wambai ya yi zargin cewa gwamnan na Edo ya keta dokoki biyu da ka iya soke zabensa

- Jigon na APC ya kuma zargi Obaseki da karya a karkashin rantsuwa

Tsohon mataimakin shugaban APC na kasa a arewa maso tsakiya, Ahmed Suleiman Wambai ya sanar da yiwuwar kotu ta tsige Godwin Obaseki daga matsayin gwamnan jihar Edo.

Wambai ya fada ma jaridar The Sun a yayin wata hira cewa akwai dalilai biyu wadanda a kansu kotu na iya soke zaben gwamnan jihar Edo.

Jigon na APC, wanda ya nuna karfin gwiwa a kan matsayarsa, ya yi korafin cewa jam’iyyarsa za ta kwato jihar Edo bisa dalilai na fasaha.

KU KARANTA KUMA: Talaka kada ya damu da karin farashin man fetur saboda ba mota ko Janareto gareshi ba - Garba Shehu

Bar murna karenka ya kama kura: Ƙusan APC ya ƙalubalanci nasarar Obaseki
Bar murna karenka ya kama kura: Ƙusan APC ya ƙalubalanci nasarar Obaseki Hoto: Nairaland Forum
Asali: UGC

Jigon na APC ya ce:

“Obaseki bai da takarda sannan muna jiran ganin gwamnan, wata kotu ko gwamnati da za ta tabbatar da cewa Obaseki ya cancanta.”

Wambai ya kuma bayyana cewa ana iya soke zaben Obaseki saboda zargin cewa ya saba wani hukunci na kotun koli ta hanyar yin karya a rantsuwa da kuma karban takardar nuna ra’ayin takara daga jam’iyyun siyasa biyu.

A kan korafinsa, jigon na APC ya bayyana nasarar da PDP ta samu a zaben Edo a matsayin na wucin gadi.

KU KARANTA KUMA: Bidiyo: Abubuwan al'ajabi da baku sani ba game da Shugaba Buhari

A wani labarin, Jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) ta karyata zargin cewa tayi watsi da dan takaranta a zaben shugaban kasan 2019, Atiku Abubakar, domin zaben wani a 2023.

Daily Sun ta ruwaito cewa shugaban uwar jam'iyyar, Uche Secondus, ya karyata labarin bayan ganawarsa da wasu gwamnonin jam'iyyar a Bauchi.

Secondus ya ce jam'iyyar za ta tabbatar da cewa duk wanda ya cancanci takara zai iya ba tare da tsangwama ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel