Zaben Edo: Ba kullum ake kwana a gado ba inji Adams Oshiomhole
- Adams Oshiomhole ya ce duk da APC sun rasa gwamna a Edo, da sauransa
- Oshiomhole ya ce har yanzu karshensa ba ta zo ba kamar yadda ake tunani
- Tsohon Gwmnan bai yi magana kan masu ganin laifinsa a rashin nasarar ba
Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, ya yi magana game da sakamakon zaben gwamnan jihar Edo da aka yi a makon jiya.
Kwamred Adams Oshiomhole ya fito a karon farko ya yi magana a kan zaben da jam’iyyarsa da ‘dan takararsa su ka sha kashi ne bayan kwana uku.
Tsohon gwamnan na jihar Edo, ya ce irin wannan rashin nasara ta na cikin gwagwarmayar rayuwa.
KU KARANTA: Ka-ka-gidan Oshiomhole a APC ya taimakawa PDP a zaben Edo
Da ya ke magana a ranar Laraba, 24 ga watan Satumba, 2020, Oshiomhole, ya nuna cewa har yanzu siyasarsa ba ta zo karshe ba kamar yadda ake rayawa.
A wani bidiyo da tsohon gwamnan ya dauka a wurin atisaye a gidansa, ya ajiye siyasa a gefe, inda ya zama malamin darashin rayuwa ya na bayani a kan kaddara.
“”A rayuwa za ka yi kokarinka ne ka bar wa Ubangiji ikon lamari. Kai dai ka yi iya yinka, ka kuma yarda da Ubangiji ya sa maka albarka.” Inji Oshiomhole.
Oshiomhole ya kuma bayyana cewa ko kadan shan kasan da jam’iyyar APC ta yi a zaben da aka yi ranar Asabar, 19 ga watan Satumban nan, bai karya shi ba.
KU KARANTA: Jigon APC ya zargi Oshiomhole da Tinubu da jawo rashin nasara
‘Dan siyasar ya ce: “Lafiya lau na ke ji, ina jin cewa da karfina. Na godewa Ubangiji. A rayuwa, wata rana za ka yi nasara, wata rana kuma za ka sha kashi.”
“Haka rayuwa ta ke.” Inji sa.
A karshe tsohon jagoran ‘yan kwadagon ya ce, “Mutane da-dama za su rika tunanin na kai kasa. Amma ina nan. Ubangiji bai ce na yi kasa ba, ban yi kasa ba.”
A baya kun ji cewa gwamna mai-nasara, Godwin Obaseki, ya ce muddin tsohon ubangidansa, Adams Oshiomhole bai ajiye kayan fadansa ba, zai yi maganinsa a siyasa.
Zababben gwamnan na Edo ya sha alwashin casa Adams Oshiomhole idan ya taso masa.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng