PDP ta aikawa Obaseki muhimmin saƙo, ta faɗa masa yadda zai yi mu'amala da abokan hamayya

PDP ta aikawa Obaseki muhimmin saƙo, ta faɗa masa yadda zai yi mu'amala da abokan hamayya

- Gwamna Obaseki ya ziyarci Shugaban PDP a Abuja kan nasarar da ya samu a zabe

- Shugaban PDP na kasa, Uche Secondus, ya shawarci Obaseki da ya zauna lafiya da abokan hamayya a jihar

- Sai dai Obaseki, ya yi alkawarin cewa ba zai bar PDP zuwa APC ba

Uche Secondus, shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya shawarci Gwamna Godwin Obaseki na Edo da ya zauna lafiya da abokan hamayya a jihar wadanda ke da muradin aiki tare da shi.

Jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito cewa Secondus ya bayar da shawarar ne a lokacin da ya jagoranci masu ruwa da tsaki na PDP a Edo domin mika godiya a sakatariyar jam’iyyar ta kasa da ke Abuja, a ranar Litinin, 5 ga watan Oktoba.

Legit.ng ta tattaro cewa Shugaban jam’iyyar ya kuma tunatar da Obaseki cewa zaben ya wuce kuma yanzu ne lokacin hada kan al’umma ciki harda “wadanda suka yi maka laifi.”

KU KARANTA KUMA: Yan kwanaki kafin zaben gwamnan Ondo: An yi harbe-harbe a garin Akure

PDP ta aikawa Obaseki muhimmin saƙo, ta faɗa masa yadda zai yi mu'amala da abokan hamayya
PDP ta aikawa Obaseki muhimmin saƙo, ta faɗa masa yadda zai yi mu'amala da abokan hamayya Hoto: @GovernorObaseki
Asali: Twitter

Secondus ya ce jam’iyyar ta samu karbuwa a wajen yan Najeriya, inda ya yi misali da jihar Ribas inda ya ce jam’iyyar adawa na hada hannu da jam’iyya mai mulki a kullun.

Ya yi bayanin cewa alamar dan siyasa na gari shine ya iya hada kan mutane da kuma aikin da kowa zai gamsu.

A martaninsa, Obaseki, wanda ya koma PDP daga APC kafin zaben ranar 19 ga watan Satumba, ya yi alkawarin cewa zai sakawa PDP da karamcin da tayi masa ta hanyar yi mata biyayya.

KU KARANTA KUMA: Yanzu yanzu: Buhari ya amince a ƙarawa malamai albashi da shekarun aiki

A wani labari na daban, PDP ta gargadi gwamnan jihar Yobe kuma Shugaban rikon kwarya na jam’ iyyar APC, Mai Mala Buni da ya daina zagin gwamnoninta.

Babbar jam’iyyar adawar a wasu jerin wallafa da ta yi a shafinta na Twitter a ranar 4 ga watan Oktoba, ta gargadi gwamnan da ya daina aiko wasu mutane a APC.

Domin su zagi gwamnoni da sauran shugabanninsu don kawai su janye hankalin mutane daga gazawa da matsalolin jam’iyyar mai mulki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng