Na yi babban laifi ga Ubangiji idan ban yi wa Wike godiya ba - Obaseki

Na yi babban laifi ga Ubangiji idan ban yi wa Wike godiya ba - Obaseki

- Godwin Obaseki na jihar Edo, ya nuna murnarsa tare da godiyarsa ga Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas

- Obaseki ya bayyana cewa, babban zunubi zai zame masa a wurin Ubangiji idan bai yi godiya ga Wike ba

- Ya ce guguwa ce ta tashi za ta hadiyesa, Wike ne ya rungumosa, ya sauya masa kaya kuma ya bashi abinci

Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya mika godiyarsa ga Nyesom Wike a kan rawar da ya taka yayin zaben gwamnan jihar da ya gabata a ranar Asabar.

Obaseki wanda ya ziyarci Wike a ranar Laraba, 23 ga watan Satumba, ya ce Gwamna Wike ya rungumo shi bayan an yi masa kora da hali daga jam'iyyar APC.

Ya bayyana cewa, kwamitin yakin neman zabensa sun hadu a gidan Wike domin duba yadda za su samu nasara a zaben da aka yi ranar Asabar da ta gabata.

Kamar yadda kwamishinan yada labarai na jihar Ribas, Paulinus Nsirim, ya sanar, Obaseki ya ce, "Bayan kora da hali da aka yi min daga tsohuwar jam'iyyata, wannan gidan ne na fara zuwa domin neman mafita.

"Ka karbeni a matsayin dan uwa, a cikin guguwa ka sauya min kaya kuma ka bani abinci.

"A wannan gidan ne kwamitin kamfen dina suka hadu domin samo hanyar nasara. Ka tattaro jama'arka a dukkan fadin kasar nan. Ka tseratar da ni daga hari da cin mutunci. Ka goyi bayanmu kuma mun yi nasara."

Ya kara da cewa, "Babban zunubi ne a tsakanina da Ubangiji idan ban yi masa godiya ba. Hatta wannan nasarar daga shi ne. Ya yi amfani ne da jama'a irinku ya tabbatar da ita."

KU KARANTA: Garar N30 a Kano: Bayan shekara daya, gidan cin abincin ya kasa cigaba da aiki

Na yi babban laifi ga Ubangiji idan ban yi wa Wike godiya ba - Obaseki
Na yi babban laifi ga Ubangiji idan ban yi wa Wike godiya ba - Obaseki. Hoto daga @punch
Asali: UGC

KU KARANTA: Hotunan yadda aka yi addu'ar ukun marigayi Sarki Zazzau, Alhaji Shehu Idris

A wani labari na daban, dan takarar gwamna a karkashin jam'iyyar APC a zaben jihar Edo da ya gabata, Fasto Ize-Iyamu, ya yi kira ga Gwamna Godwin Obaseki wanda ya kayar da shi a zabe, da ya dawo APC.

A wata tattaunawar da aka yi da Ize-Iyamu a wani gidan talabijin a ranar Laraba, ya ce," Za mu yi magana da kowa kuma zamu dawo da kowa. Ina son mika sakon gaisuwata ga dan uwana, gwamna. Ina kira garesa da ya dawo jam'iyya. A kowanne wuri ana samun hargitsi.

"Bai kamata a ce wata rashin jituwa ce ta sa ya bar gida ba. Na yi kuskure a da kuma na gane cewa babban kuskure ne. Ba zan so a matsayinsa na babban yayana ya yi irin wannan kuskuren ba.

"Ina so in yi kira garesa da ya ajiye fushinsa kuma ya dawo gida. A APC, za a dubesa a matsayin shugaba, wanda akwai matukar wuya hakan ta kasance a sabuwar jam'iyyarsa."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel