Wasu jiga-jigan jam'iyyar APC sun marawa Obaseki baya saboda 2023 - Kakakin Tinubu

Wasu jiga-jigan jam'iyyar APC sun marawa Obaseki baya saboda 2023 - Kakakin Tinubu

- Mista Tunde Rahman, mai magana da yawun jagoran jam'iyyar APC na kasa Bola Tinubu ya ce wasu jiga-jigan jam'iyyar suna da hannu a kayen da ta sha a zaben gwamnan Edo

- Tunde Rahman ya yi ikirarin cewa akwai wasu kusoshin jam'iyyar da yanzu batun takarar shugabancin kasa na 2023 suka saka a gaba kuma suna ganin Tinubu zai iya kawo musu cikas

- Duk da cewa jigon jam'iyyar mai mulki bai taba tabbatar da cewa zai fito takarar ba, wasu 'yan siyasan jam'iyyar sun fara nuna cewa za su goyi bayansa idan ya fito

Tunde Rahman, kakakin jagoran jam'iyyar APC na kasa, Bola Tinubu ya ce wasu daga cikin kusoshin jam'iyyar APC sun goyi bayan Gwamna Godwin Obaseki na jam'iyyar PDP a zaben gwamnan jihar Edo saboda siyasar 2023.

Rahman ya bayyana hakan ne cikin wani rubutu da ya wallafa mai taken, 'Asiwaju Tinubu da Zaben Edo', da The Cable ta wallafa.

DUBA WANNAN: Mutum 30 sun mutu a harin da ISWAP ta kai wa tawagar gwamnan Borno

Wasu kusoshin jam'iyyar APC sun marawa Obaseki baya saboda 2023 - Kakakin Tinubu
Wasu kusoshin jam'iyyar APC sun marawa Obaseki baya saboda 2023 - Kakakin Tinubu. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

Ana rade-radin cewa Tinubu na da niyyar fitowa takarar shugaban kasa a shekarar 2023 amma bai taba tabbatar da hakan ba ko ya musanta.

KU KARANTA: Yadda aka kashe jami'in DSS a Plateau

Sai dai, an cewa wasu 'yan siyasa da dama a jam'iyyar ta APC da ke sha'awar fitowa takarar suna kokarin dakile yiwuwar fitowa takararsa.

"Ya zama dole a bayyana cewa duk wannan hayaniyar da ake yi bayan zabe Edo na kananan maganganu, bata suna, munafinci duk dan batun 2023 ne.

"A maimakon su mayar da hankali wurin karfafa jam'iyyarsu su tabbatar da lashe zabe su kuma rika biyaya ga dokokin jam'iyya, wasu kusoshin jam'iyyar APC suna ta yi wa jam'iyyar zagon kasa da niyyar tarwatsa da sunan siyasar 2023.

"Amma kamar yadda Asiwaju ya fada, shi mutum ne kamar kowa kuma bai san gaibu ba. Allah ne kadai ya san abinda zai faru a 2023."

A wani rahoton, dan majalisa mai wakiltar Oyo ta Arewa, Sanata Abdulfatai Buhari ya ce zai goyi bayan jagoran jam'iyyar APC, Bola Tinubu idan ya nuna sha'awar fitowa takarar shugabancin kasa a Najeriya.

Buhari ya bayyana hakan ne yayin hirar da ya yi da wani dan jarida, Edmund Obilo a ranar Alhamis kamar yadda The Punch ta ruwaito. Read more:

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel