Bayan shan mugun kaye, Ize-Iyamu na jam'iyyar APC ya aike wa Obaseki muhimmin sako
- Dan takarar jam'iyyar APC a zaben Edo da ya gabata, Fasto Ize-Iyamu, ya aike wa Obaseki muhimmin sako
- Kamar yadda Faston yace, ana iya samun rikici a kowanne gida, amma yanke shawarar barin gidan bai kamata
- Ya yi kira garesa a matsayinsa na babban yayansa, da ya garzayo ya dawo gida APC domin nan ne tushensa
Dan takarar gwamna a karkashin jam'iyyar APC a zaben jihar Edo da ya gabata, Fasto Ize-Iyamu, ya yi kira ga Gwamna Godwin Obaseki wanda ya kayar da shi a zabe, da ya dawo APC.
A wata tattaunawar da aka yi da Ize-Iyamu a wani gidan talabijin a ranar Laraba, ya ce," Za mu yi magana da kowa kuma zamu dawo da kowa. Ina son mika sakon gaisuwata ga dan uwana, gwamna. Ina kira garesa da ya dawo jam'iyya. A kowanne wuri ana samun hargitsi.
"Bai kamata a ce wata rashin jituwa ce ta sa ya bar gida ba. Na yi kuskure a da kuma na gane cewa babban kuskure ne. Ba zan so a matsayinsa na babban yayana ya yi irin wannan kuskuren ba.
"Ina so in yi kira garesa da ya ajiye fushinsa kuma ya dawo gida. A APC, za a dubesa a matsayin shugaba, wanda akwai matukar wuya hakan ta kasance a sabuwar jam'iyyarsa."
KU KARANTA: Garar N30 a Kano: Bayan shekara daya, gidan cin abincin ya kasa cigaba da aiki
KU KARANTA: Zamfara: Yadda dan majalisa ya gwangwaje tsoffin malamansa da sha tara ta arziki
A wwani labari na daban, dan takarar gwamnan jihar Edo a karkashin inuwar jam'iyyar APC, Fasto Osagie Ize-Iyamu, ya fitar da takarda bayan lallasa shi da Gwamna Obaseki na jam'iyyar PDP yayi a zaben da ya gabata.
Obaseki ya samu kuri'u 307,955 inda ya kayar da babban abokin adawarsa, Ize-Iyamu, wanda ya samu kuri'u 223,619.
A martanin da ya fitar bayan hukumar zabe mai zaman kanta ta sanar da nasarar Obaseki, Ize-Iyamu ya mika godiyarsa ga magoya bayansa a kan kokarin da suka yi masa yayin zaben.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng