Kwankwaso ya ce barazanar UK da Amurka ta yi maganin masu magudin zabe

Kwankwaso ya ce barazanar UK da Amurka ta yi maganin masu magudin zabe

- Rabiu Kwankwaso ya yi magana bayan Jam’iyyar PDP ta lashe zaben Jihar Edo

- Babban Jigon Jam’iyyar ya taya Godwin Obaseki nasarar zarcewa a kan mulki

- Tsohon Gwamnan ya ce barazanar wasu kasashen waje sun taimaka wajen zaben

Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya shiga cikin sahun wadanda su ka taya gwamna Godwin Obaseki murnar lashe zaben jihar Edo.

Rabiu Musa Kwankwaso ya fitar da wani jawabi ne ta bakin babban sakatarensa, Muhammad Inuwa Ali, a ranar Litinin 22 ga watan Satumba, 2020.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana sakamakon zaben Edo a matsayin nasara ga duk wani wanda ya yi imani da tsarin damukaradiyya a Najeriya.

‘Dan siyasar ya ce maganganun da kasashen Birtaniya da Amurka su ka yi ya razana masu magudi.

KU KARANTA: Fayose ya taya Godwin Obaseki da PDP murnar lashe zabe

A cewar tsohon Sanatan, shelar da su ka fito daga manyan Duniya a wajen Najeriya sun yi tasiri wajen takawa masu tafka magudi da niyyar murde zabe burki.

Da ya ke magana ta bakin hadimin na sa, Rabiu Kwankwaso ya ce:

“Bari in godewa wakilan kasashen waje a Najeriya, musamman jakadancin Amurka da Birtaniya a Najeriya da shawarwarinsu a kan kari ga masu shirya magudi da murdiyar zabe da tada rigima.”

“Shawarar ku ga masu magudi da jawo rikicin zabe na cewa akwai hukunci na danyen aikinsu a wajen iyakokin Najeriya ya yi aiki.” Inji tsohon ministan kasar.

KU KARANTA: Abin da ya kai Shugaban Kwankwasiyya zuwa Edo

Kwankwaso ya ce barazanar UK da Amurka ta yi maganin masu magudin zabe
Tsohon Gwamnan Kano Rabiu Kwankwaso
Asali: Depositphotos

Injiniya Kwankwaso ya kare da: “Mun gode maku da ku ka karfafa damukaradiyya a kasarmu.”

A jawabinsa, ya jinjinawa gwamna Nyesom Wike na kokarin da ya yi wajen ganin PDP ta yi nasara. Haka zalika ya yabawa shugabannin PDP da mutanen Edo.

Kafin zabe kun samu labarin cewa PDP ta tura Kwankwaso zuwa Edo inda ya taimakawa gwamna Godwin Obaseki wajen jawo masa kuri’un Hausawan da ke jihar.

Kamar yadda hadiminsa ya bayyana, Kwankwaso ya kaddamar da wasu ayyukan gwamna Obaseki.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng