Zaben Edo: Jam'iyyar NCP ta buƙaci a soke zaɓe, a hukunta Obaseki

Zaben Edo: Jam'iyyar NCP ta buƙaci a soke zaɓe, a hukunta Obaseki

- Sabon tashin hankali ya kunno kai a jihar Edo bayan zabe

- Jam’iyyar NCP ta yi kira ga soke zaben gwamnan da aka gudanar a ranar Asabar, 19 ga watan Satumba

- Jam’iyyar ta yi ikirarin cewa babu sunanta da alamarta a takardar INEC

Sabon tashin hankali ya kunno kai a Edo yayinda Peters Osawaru Omiragbon, dan takarar jam’iyyar National Conscience Party (NCP) a zaben da aka kammala, ya nemi a soke zaben gwamnan.

An gudanar da zaben na Edo a ranar Asabar, 19 ga watan Satumba, a fadin kananan hukumomi 18 da ke jihar inda masu zabe suka yi turuwan fitowa don zabar jagoransu.

Gwamna Godwin Obaseki ne ya lashe zaben, inda ya kayar da dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) Osagie Ize-Iyamu da sauran yan takara 12.

Hukumar zabe ta kaddamar da gwamnan na Edo a matsayin wanda ya lashe zaben bayan ya hada dukkanin abunda ake bukata da kuri’u 307,955.

KU KARANTA KUMA: Yunƙurin fatattakar Oshiomhole daga APC: Jigon PDP ya roƙi APC ta ɗaga mashi ƙafa

Zaben Edo: Jam'iyyar NCP ta buƙaci a soke zaɓe, a hukunta Obaseki
Zaben Edo: Jam'iyyar NCP ta buƙaci a soke zaɓe, a hukunta Obaseki Hoto: Daily Sun
Asali: UGC

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, Dele Momodu, da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan sun bayyana nasararsa a matsayin nasara ga damokradiyya.

Ana haka kawai, sai Omoragbon ya nemi a soke zaben kan abunda ya bayyana a matsayin cire logon jam’iyyarsa da sunansa a takardar zaben da INEC tayi ba bisa ka’ida ba.

INEC a watan Fabrairu ta cire sunayen jam’iyyun siyasa 74 - wanda a ciki harda NCP.

Koda dai har yanzu akwai jayayyar doka kan matakin hukumar inda kotunan daukaka kara biyu suka zartar da hukunci da yayi karo da juna kan janye rijistan.

Omoragbon ya bukaci Gwamna Obaseki da ya yi murabus cikin girma maimakon kotu ta tsige shi sannan kuma fuskantar yiwuwar zuwa gidan yari na shekaru biyu kan take dokar zabe.

KU KARANTA KUMA: Idan aka bani dama: Ina da burin zama shugaban kasar Nigeria a 2023 - Okorocha

A gefe guda, zaben kujerar gwamnan jihar Edo ya zo kuma ya tafi amma har yanzu akwai sauran barbashin kura tsakanin yan siyasa da masu sharhi kan lamuran yau da kullum.

Duk da cewa jam'iyyun siyasa 14 sukayi takara a zaben, sakamakon ya nuna cewa takaran na tsakanin jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP da All Progressives Congress APC.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel