Zaben Edo: An kafa kotun sauraron korafe korafen zabe daga APC da sauran jam'iyyu
- An kafa kotun zabe domin duba karar da yan takara ka iya shigarwa game da zaben da aka kammala kwanan nan
- Kotun zaben za ta yi zama ne a harabar babbar kotun da ke jihar Edo
- Zuwa yanzu dai jam’iyyar APC bata nuna aniyar kalubalantar sakamakon zaben na Edo ba
Yan kwanaki bayan kaddamar da Godwin Obaseki a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Edo, shugabar kotun daukaka kara, Justis Monica Dongban-Menem ta kafa kotun sauraron karar zabe domin duba kararrakin da zai fito daga zaben.
A cewar jaridar The Nation, an tsara zaman sauraron kararrakin zaben a harabar babbar kotun da ke Benin, babbar birnin jihar Edo.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren kotun zaben, Sunday Martins ya fitar a ranar Talata, 22 ga watan Satumba.
KU KARANTA KUMA: Obaseki: Ba ni da niyyar komawa APC, ina cikin PDP daram
“Ana sanar da jama’a cewa mai girma shugabar kotun daukaka kara ta Najeriya, Justis M. B Dongban Mensem ta kafa kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan da aka gudanar a jihar Edo.”
KU KARANTA KUMA: Bayan cin zaben Edo: Obaseki ya yiwa Buhari godiya na bunkasa fannin zabe a Najeriya
Jawabin ya ci gaba da bayyana cewa shugaban alkalai na jihar Edo, Justis Edigin ya amince da amfani da dakin sauraron kararrakin zabe da ke harabar babbar kotu a Sapele Road, birnin Benin don sauraron korafe-korafen.
Legit.ng ta tuna cewa Obaseki na PDP ya kayar da Ize-Iyamu na APC a zaben.
Sai dai Ize-Iyamu wanda yace har yanzu yana nazarin sakamakon zaben ne bai bayyana ko zai kalubalanci sakamakon ba a kotu.
A geefe guda, hukumar INEC ta bada shahadar nasara a zabe ga gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, da mataimakinsa, Philip Shaibu, a matsayin wadanda sukayi nasara.
Da wannan shahadar, Obaseki da Shaibu sun cika sharrudan dokar zabe domin rantsar da su ranar 12 ga Nuwamba, 2020 a Benin City domin wa'adinsu na biyu a ofis.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng