Obaseki: Ba ni da niyyar komawa APC, ina cikin PDP daram
- Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya yi magana game da yiwuwar komawarsa APC
- Obaseki wanda aka sake zaba a matsayin gwamnan Edo karo na biyu karkashin PDP ya ce ko kadan baya tunanin komawa tsohuwar jam’iyyarsa
- Ya ce babu adalci idan har ya sauya sheka daga PDP wacce ta bashi damar cimma burinsa
Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya bayyana cewa bai da niyyar sauya sheka daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Ku tuna cewa Obaseki ya koma PDP ne bayan jam’iyyar APC ta hana shi sake takara a karkashin inuwarta.
A zaben da aka gudanar a ranar Asabar, 19 ga watan Satumba, Obaseki ya yi nasara bayan ya kayar da babban abokin hamayyarsa, Osagie Ize-Iyamu na APC.
KU KARANTA KUMA: Bayan cin zaben Edo: Obaseki ya yiwa Buhari godiya na bunkasa fannin zabe a Najeriya
Gwamnan ya samu kuri’u 307,955 yayinda dan takarar jam’iyyar adawa ta jihar ya samu kuri’u 223,619.
Da yake jawabi a shirin safe na Arise TV, gwamnan ya ce ya daukar wa mutanen Edo alkawari a matsayin dan takarar PDP kuma zai zama rashin Adalci idan ya bar jam’iyyar bayan ya cimma kudirinsa na zarcewa.
“Ba daidai bane kaurace masu, ba ni da niyyar komawa APC,” in ji shi.
A gefe guda, Gwamna Godwin Obaseki, ya ce jagoran jam'iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, da ire irensa, barazana ne ga demokaradiyyar Nigeria.
Obaseki ya bayyana hakan a ranar Talata a tattaunawa da shi cikin 'Shirin Safiya' na gidan talabijin din Arise TV, wata kafar watsa labarai ta jaridar THISDAY.
KU KARANTA KUMA: Lekan Ojo ya daurawa Tinubu da Oshiomhole laifin shan kashi a hanun PDP
Da ya ke bayyana tsohon gwamnan jihar Lagos da ire irensa a matsayin 'yan wasa, Obaseki ya ce suna wasa da demokaradiyyar kasar ne, hakan kuma babbar illa ce.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng