Siyasar Edo: APC na kira a hukunta Hadimin Obaseki saboda ‘zargin kisa’

Siyasar Edo: APC na kira a hukunta Hadimin Obaseki saboda ‘zargin kisa’

- APC a Edo ta bayyana cewa da zubar da jini Jam’iyyar PDP ta lashe zabe

- Jam’iyyar APC ta ce an rika harbe mutane da umarnin wasu manyan PDP

- Don haka ne Jam’iyyar ta nemi a kama wani Mai ba gwamnan Edo shawara

Jam’iyyar APC ta reshen jihar Edo, ta yi kira ga Sufeta Janar na ‘yan sanda, Mohammed Abubakar Adamu, ya kama wani babban hadimin gwamnan Edo.

APC ta bukaci IGP Mohammed Abubakar Adamu ya bada umarnin hukunta wani hadimin gwamna Godwin Obaseki da ake zargi da hannu a kisan-kai.

Jam’iyyar adawar ta na zargin Hadimin gwamnan na jihar Edo ne ya bada umarnin a harbe wata ‘yar jam’iyyar APC mai suna Yado Odogbo a garin Ovia.

KU KARANTA: Wanene Gwamna Obaseki da ya doke Oshiomhole da APC a Edo?

Wannan mummunan lamari ya auku ne lokacin zaben gwamna a cikin unguwar Nikorogha, da ke karamar hukumar Ovia ta Kudu maso yamma, a jihar Edo.

Jawabin da jam’iyyar APC ta yi, ya fito ne ta bakin darektan yada labarai na kwamitin yakin neman zaben Fasto Osagie Ize-Iyamu, Mista John Mayaki a makon nan.

John Mayaki ya ce kisan wannan Baiwar Allah kadan ne daga cikin ta’adin da PDP mai mulki ta yi a yankuna da-dama na jihar Edo domin ta koma kan mulki.

Ya ce: ““Daga Uhunmwode, Urhonigbe ta Arewa, zuwa kananan hukumomin Orhionmwon, Oredo, Egor, da kuma Ikpoba-Okha, jami’an zabe sun tsere…”

KU KARANTA: An rasa rai yayin da ake zanga-zanga saboda matsalar tsaro

Siyasar Edo: APC na kira a hukunta Hadimin Obaseki bisa ‘zargin kisa’
Obaseki da Ize-Iyamu Hoto: Sun
Asali: UGC

Mayaki ya cigaba da bayanin yadda aka yi ta’adi: “Yayin da masu kada kuri’a su ka tserewa rayuwarsu a sakamakon harbe-harben da jami’an PDP su ka rika yi”

Jam’iyyar ta ce ya zama dole a biya jinin Odogbo, wanda aka kashe ba tare da hakki ba. “Mun yi duk abin da za mu iya na ganin ba mu dauki doka a hannunmu ba.”

“A ‘yan kwanakin bayan nan¸ Ize-Iyamu ya na ta kokarin kai ziyara domin yi wa iyalan wadanda aka kashe, da wadanda aka yi wa rauni ta’aziyya.” Inji kakakin APC.

A makonnin da su ka wuce ne INEC ta sanar da Godwin Obaseki a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Edo wanda aka yi a ranar 19 ga watan Satumba.

A wannan karo ma babban abokin hammayar gwamnan, Fasto Ize-Iyamu ya zo na biyu ne.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng