Shugaban Jam’iyyar APC ya fadawa Godwin Obaseki ya yi murabus a jihar Edo
-Jam’iyyar APC ta zargi Gwamna Godwin Obaseki da rashin iya mulki
-Shugaban APC, ya bukaci Gwamnan jihar ya rubuta takardar murabus
-APC ta zargi Obaseki da laftowa Gwamnatin Edo bashi da rashin tsaro
Shugaban jam’iyyar APC na rikon kwarya a jihar Edo, Kanal David Imuse, ya fito ya yi kaca-kaca da salon mulkin gwamna Godwin Obaseki.
Jaridar Vanguard ta fitar da rahoto cewa David Imuse ya bukaci Mai girma gwamna Godwin Obaseki ya yi murabus, ya bar wa wani kujerar.
A ranar Lahadi, 20 ga watan Disamba, 2020, Kanal Imuse ya yi wannan kira, ya ce Godwin Obaseki bai san abin da yake yi a ofishin gwamna ba.
A cewar shugaban jam’iyyar hamayyar ta APC, dabaru sun karewa gwamnatin Obaseki a jihar Edo.
KU KARANTA: Abubuwan da su ka ba PDP nasara a zaben Edo
Ganin yadda bashin da ke kan gwamnatin Edo ya ke kara taruwa, jam’iyyar APC ta na ganin babu abin da ya fi irin Mista Obaseki ya ajiye mulki.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Bayan haka, jam’iyyar APC mai adawa a Edo, ta na kukan halin rashin tsaro da ake fama da shi, tare da zargin gwamnatin Obaseki da saba doka.
Hakan na zuwa ne a lokacin da ake yawan samun sace-sace da tashin-tashina tun da aka samu wasu marasa gaskiya da su ka tsere daga kurkuku.
Jaridar Premium Times ta yi yunkurin jin ta-bakin gwamnan bayan kiran da David Imuse ya yi, amma Godwin Obaseki bai amsa kiran wayarsa ba.
KU KARANTA: Takaitaccen tarihin Godwin Obaseki
Tuni shugaban PDP na Edo, Chris Nehikhare ya yi wa takwaransa na jam’iyyar APC raddi, ya ce bai kamata ya rika yin irin wadannan kalamai ba.
2023: Kura Ta Kara Turnuke Wa Atiku, Shugabannin PDP a Wata Jiha Sun Yi Fatali da Sunayen Tawagar Kamfe
Kwanki gwamna Godwin Obaseki ya yi wa tsohon Mai gidansa, Adams Oshiomhole gorin kudi.
Abin har ta kai Godwin Obaseki ya na bada labarin yadda su ka taimakawa Oshiomhole ya nemi kujerar gwamnan jihar Edo karkashin jam'iyyar AC.
Obaseki ya bayyana rawar da ya taka a kotu har aka karbe nasarar Oserheimen Osunbor da jam'iyyar PDP, aka ba Oshiomhole nasara a zaben Edo.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng