Har yanzu yana cikinmu: APC ta ƙaryata jita jitar fatattakar Oshiomole daga jam'iyyar kwata kwata
- Bangaren Anselm Ojezua na APC reshen Edo ya karyata batun dakatar da Adams Oshiomhole
- Jam’iyyar ta APC ta ce babu kamshin gaskiya a rade-radin cewa ta sanar da shugabancinta na kasa game da shirin dakatar da dan siyasar
- Shugaban APC a jihar Edo, Anselm Ojezua ne ya yayi karin haske kan lamarin
Kungiyar adawa ta jam’iyyar All Progress Congress (APC) a reshen Edo ta yi watsi da rahoton da ke ikirarin cewa an dakatar da Adams Oshiomhole daga jam’iyyar kan sakamakon zaben jihar.
Shugaban kungiyar adawar ta jam’iyyar APC a jihar Edo, Anselm Ojezua a ranar Talata, 22 ga watan Satumba, ya ce rahoton dakatar da Oshiomhole ba gaskiya bane.
A wata hira da jaridar The Nation tayi dashi ta wayar tarho, Ojezua ya kuma karyata cewarsa bangarensa ta rubuta wasika zuwa ga shugabancin jam’iyyar na kasa inda take sanar masa da hukuncinsu na dakatar da Oshiomhole.
KU KARANTA KUMA: Bayan cin zaben Edo: Obaseki ya yiwa Buhari godiya na bunkasa fannin zabe a Najeriya
Ojezua ya ce jam’iyyar bata riga ta sake duba sakamakon zaben gwamnan Edo ba.
“Bamu hadu ba. Za mu yi taro ne a ranar Alhamis domin sake duba lamarin gabaki daya. A sannan ne za mu yanke shawara. Bamu hadu ba. Za mu gana a ranar Alhamis (24 ga watan Satumba).”
A gefe guda, Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya yi karin haske a kan dangartakarsa da dan takarar gwamna na jam'iyyar APC, Fasto Osagie Ize-Iyamu.
Da ya ke magana a shirin Morning Show na Arise TV, Obaseki ya ce ba shi da matsala yin takara da Ize-Iyamu a zaben da aka yi a ranar Asabar 19 ga watan Satumban 2020.
KU KARANTA KUMA: Zaben Edo: An kafa kotun sauraron korafe korafen zabe daga APC da sauran jam'iyyu
Amma gwamnan ya ce yana da matsala da wasu mutane a jam'iyyar ta APC da suka kusa da dan takarar ciki har da tsohon shugaban jam'iyyar Adams Oshiomhole.
A hirarsa da BBC a ranar Lahadi, bayan an sanar da nasararsa, gwamnan ya fada wa Ize-Iyamu cewa mutane sun nuna masa cewa lokaci ya yi da zai tafi ya yi wani abin daban.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng