Bayan cin zaben Edo: Obaseki ya yiwa Buhari godiya na bunkasa fannin zabe a Najeriya

Bayan cin zaben Edo: Obaseki ya yiwa Buhari godiya na bunkasa fannin zabe a Najeriya

- Godwin Obaseki ya kara mika sakon godiya zuwa ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari

- Zababben gwamnan na Edo a karo na biyu ya ce nasararsa ta tabbata ne saboda Buhari ya bayar da fili kowa ya baje ‘kanjinsa

- Obaseki ya ce Shugaban kasar ya umurci INEC da yan sanda da su yi aikinsu ba tare da hada kai da kowace jam’iyyar siyasa ba

Godwin Obaseki ya yi jinjina ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari kan zaben gwamnan Edo, ya bayyana cewa ya yi nasarar lashe zaben na ranar Asabar, 19 ga watan Satumba ne saboda adalcinsa.

Da yake jawabi a wata hira da sashin BBC a ranar Lahadi, 20 ga watan Satumba, bayan kaddamar dashi a matsayin wanda ya lashe zabe, Obaseki ya ce rashin son kai da Shugaban kasar ne ya sa shi yin nasara.

KU KARANTA KUMA: Lekan Ojo ya daurawa Tinubu da Oshiomhole laifin shan kashi a hanun PDP

Gwamnan ya bayyana cewa kafin zaben, shugaba Buhari ya fitar da wani jawabi inda ya yi kakkausar gargadin cewa ya zama dole a ba dukkanin yan takara fili su fafata da kyau.

Bayan cin zaben Edo: Obaseki ya yiwa Buhari godiya na bunkasa fannin zabe a Najeriya
Bayan cin zaben Edo: Obaseki ya yiwa Buhari godiya na bunkasa fannin zabe a Najeriya Hoto: Clacified/ICIR
Source: UGC

“Kafin zaben, Shugaban kasar ya fitar da wata sanarwa cewa kowa yayi aikinsa yadda ya kamata, cewa a bari kowace jam’iyya ta taka rawarta.

“Shugaban kasar ya kuma umurci INEC da sufeto janar na yan sanda da su yi aikinsu kuma sun yi aikinsu bisa gaskiya,” in ji gwamnan.

Legit.ng ta tuna cewa bayan an shafe watanni ana fama, Gwamna Godwin Obaseki ya yi nasarar kayar da Ize-Iyamu.

KU KARANTA KUMA: Bayan cin zaben Edo: Obaseki ya aike da sako ga Tinubu, Oshiomhole da ire irensu

Manyan yan Najeriya irin su Atiku Abubakar, tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan sun bayyana nasarar Obaseki a matsayin nasara ga damokradiyya.

A wani labarin, Godwin Obaseki, ya sha alwashin gasa wa tsohon ubangidansa, Adams Oshiomhole aya a hannu idan har ya ci gaba da “sakin zakunansa.”

A tuna cewa akwai gabar siyasa a tsakanin Obaseki da Oshiomhole tun a 2019.

Hakan ya sa gwamnan ya sauya sheka daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa Peoples Democratic Party (PDP) a watan Yunin 2020.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel