Matsin tattalin arziki
Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya yi fatali da hukuncin Kotun Koli kan ƴancin kananan hukumomi a Najeriya inda ya ce yunwa ya kamata a kawar a wannan lokaci.
Sheikh Adam Muhammad Albanin Gombe ya ce a shirye yake da duk wani maras kunya da zai tunkari malami a kan mimbari kan hana zanga zanga yayin hudubar Jumu'a.
Ana tsaka da cece-kuce kan cewa kusoshin gwamnati ba sa iya ganawa da shugaban kasa, Bola Tinubu, gwamnan jihar Gombe Inuwa Yahaya ya samu ganinsa a ranar Juma'a.
Gwamnatin tarayya ta amice da kafa kwamiti domin yaki da yunwa a Najeriya. Sanata Kashim Shettima ne ya kaddamar da kwamitin a fadar shugaban kasa a yau.
Wata kungiyar dalibai ta yi martani ga Sanata Ali Ndume bayan ya ce akwai yunwa da wahalhalu a Najeriya kuma shugaba Bola Tinubu ya gagara tabuka komai kan lamarin
Gwamnan bankin Najeriya (CBN), Yemi Cardoso, ya ce Najeriya na fuskantar tsadar kayayyaki ne sakamakon bashin Naira tiriliyan 37.5 da aka baiwa gwamnatin tarayya
Gwamnatin jihar Zamfara ta amince da fitar biliyoyin Naira domin gina tashar motar zamani a Gusau, inda ake sa ran kashe akalla N4,854,135,954.53.
Yayin da 'yan Najeriya ke kukan yunwa, ministan noma da samar da abinci, Abubakar kyari ya bayyana ranar karyewar farashin abinci, inda ya ce saura kwanaki 180.
Sanata Ali Ndume daga jihar Borno ya koka kan cewa ba a samun ganin shugaban kasa Bola Tinubu domin ba shi shawara kan magance tsadar abinci a Najeriya.
Matsin tattalin arziki
Samu kari