Matsin tattalin arziki
'Yan gudun hijira a jihohin Niger da Borno sun roki Shugaba Bola Tinubu ya tausaya musu wurin dawo da Ministar jin kai da walwala, Dakta Betta Edu.
Gwamnatin jihar Lagos ta shirya kakaba karbar haraji kan masu ajiye ababan hawa a wuraren ibada da sauran hanyoyi wanda ake sa ran zai fara aiki a watan Oktoba.
Fitaccen malamin addinin Musulunci a jihar Gombe, Sheikh Muhammad Adam Albaniy ya yi tsokaci kan shirin raba tirelolin shinkafa inda ya ba shi ne mafita ba.
Kungiyar Arewa Progressives for Good Governance ta soki tsohon Ministan matasa, Solomong Dalung kan zargin goyon bayan zanga-zanga inda ta ce rashin adalci ne.
Bola Ahmed Tinubu ya amince a rika biyan kowane ma’aikaci akalla N70, 000 a wata. Za a ga yadda abinci zai lakume daukacin sabon albashin ma’aikaci a wata.
Jami'iyyar APC ta yi martani ga gwamnonin PDP bayan sun caccaketa kan jawo wahalar rayuwa a Najeriya, Kakakin APC, Felix Morka ya ce PDP ce babbar matsala.
Gwamnatin Mai Mala Buni ta roki al'umar jihar Yobe da su guji shiga zanga-zangar gama gari da wasu ke kokarin haɗawa a kasar nan saboda matsin tattalin arziki.
Kungiyar Ohanaeze ta kabilar Ibo ta umurci yan kabilar su nisanci zanga zanga a dukkan sassan Najeriya saboda kaucewa fadawa rikici da suka saba yi a baya.
Hukumar NOA ta ce ta gano bayanan wadanda ke daukar nauyin matasa su gudanar da zanga-zangar adawa da gwamnatin Shugaba Tinubu kan matsin tattalin arziki.
Matsin tattalin arziki
Samu kari