Matsin tattalin arziki
Diyar Shugaba Bola Tinubu na Najeriya, Folashade Tinubu ta yi magana kan shirin da matasa ke yi a kasar inda ta ce shiga lamarin bai zai haifar da 'da mai ido ba.
'Yan Najeriya sun yi karo karo, sun ba da tallafin N1m ga Ismail Lasisi da Lukman Adeyemi, mutanen da aka gano ba su da laifi bayan shafe shekara 24 a gidan yari.
Duk da matasan kasar nan sun bayyana cewa za su gudanar da zanga-zangar lumana a cikin kwanaki 10, yan kasuwa sun dauki matakin ba wa shagunansu da ke Kano tsaro.
Ministan Abuja, Nyesom Wike ya zargi wasu 'yan siyasa da ba su yi nasara a zabe da shirya wannan zanga-zanga domin kifar da gwamnatin Tinubu a kasar.
Ministan ayyuka, David Umahi ya roki matasa da su hakura da zanga-zangar da suke shirin yi inda ya yi ikirarin cewa Tinubu ne silar rashin lalacewar Najeriya.
Fitaccen mai sharhi kan al'amuran al'ummar Najeriya, Farfesa Farooq Kperogi, ya bayyana hakikanin wadanda suka dauki nauyin zanga-zangar da ake shirin yi a kasar.
Sheikh Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi bai goyon bayan tsare-tsaren APC, ya ce idan Bola Tinubu ya na so a zauna lafiya komai ya tafi daidai sai ya maido tallafi.
Gwamnatin Tarayya a karyata wata sanarwa da ke yawo cewa Shugaba Bola Tinubu ya yi jawabi kan matsin tattalin arziki inda ya dawo da tallafin mai da na lantarki.
Bola Tinubu ya yi alkawarin talaka zai sarara idan ya karbi mulki. Matsin rayuwa da zargin ko-in-kula sun yi sanadiyyar da matasa za su hau titi su yi zanga-zanga.
Matsin tattalin arziki
Samu kari