Matsin tattalin arziki
Jigon APC a Kano, Nasiru Bala Ja'oji ya roki mazauna Kano da su guji fita zanga-zanga a jihar inda ya ce wasu kasasehn Afirka sun shiga matsala kan zanga-zanga.
Shugaban kungiyar Izala na kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau ya yi umurni ga limamai kan fara alkunut a fadin Najeriya. Sheikh Bala Lau ya fadi haka ne a Abuja.
Jagoran zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a Sokoto, Bashir Binji ya ajiye jagoranci bayan hango babbar barazanar tsaro wajen kai hari kasuwanni da bankuna a jihar.
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya bayyana cewa duk wanda yake sha'awar fita zanga-zanga ga fili nan ga mai doki, su kam za su zauna su ci abinci.
Bayan tattaunawa tsakanin jagororin zanga zanga da rundunar yan sanda ta kasa kan tsarin fita kan tituna a ranar Talata, an yi baram baram a tsakaninsu.
Jagororin zanga zanga a Najeriya wanda suka hada da Femi Falana, Ebun-Olu Adegboruwa da Inibehe Effiong sun mika bayanansu ga yan sanda kuma sun tattuana.
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya roki 'yan kasar nan su marawa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu baya, inda ya ce shugaban na da kyawawan manufofi.
Akalla matasa 80,000 ne suka nemi tallafin Naira biliyan 110 awanni 72 bayan bude shafin asusun tallafawa matasa na NYIF. Jamila Bio Ibrahim ta sanar da hakan.
Kungiyar Arewa Consultative Forum (ACF) ta nesanta kanta da zanga-zangar yunwa da ake shirin farawa a fadin kasar daga ranar 1 zuwa 10 ga watan Agusta.
Matsin tattalin arziki
Samu kari