Matsin tattalin arziki
Yayin da ake sa ran fara zanga-zangar gama gari a fadin Najeriya daga yau Alhamis 1-10 Agusta, 2024, wani lauya, Ebun Olu Adegboruwa ya nemi a rage kwanakin fita.
Gwamnatin Tarayya ta bayyana dalilin kin sanar da wuraren siyar da shinkafa mai nauyin 50kg kan kudi N40,000 kacal inda ta ce ta yi hakan ne domin dalilai na tsaro.
Gwamnonin jihohi sun ja kunnen masu zanga zanga su bi hankali ban da yin duk wani abu da zai iya kawo tashin tashin a tsawon lokacin da za su ɗauka.
Mawakin APC, Dauda Kahutu Rarara ya yi wakar martani bayan goge shafinsa na Facebook da talakawa suka nema a yi a kan wakar Bola Tinubu cikin sabuwar waka.
A ranar Alhamis, 1 ga watan Agusta, matasa za su hau kan tituna domin yin zanga zangar adawa da manufofin gwamnati da suka haifar da tsadar rayuwa.
Mai ba shugaban ƙaa shawara kan harkokin ɗalibai, Sunday Asefun ya ce suna zargin wasu masu ƙarfin juya gwamnati da ake ce ma Cabals da hannu a zanga zanga.
Babbar Kotun jihar Ogun ta umarci masu gudanar da zanga-zangar da su yi a wurare guda hudu kacal a jihar bayan shigar da korafi gabanta da gwamnati ta yi.
Karamin Ministan karafa a Najeriya, Uba Maigari ya roki 'yan jihar Taraba alfarma da su guji fita kan tituna domin gudanar da zanga-zanga da ake shirin yi.
Kungiyar NADECO a kasar Amurka ta gargadi gwamnatin Najeriya kan taba masu zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a Najeriya. Ta ce Tinubu ma ya yi zanga zanga a baya.
Matsin tattalin arziki
Samu kari