Matsin tattalin arziki
Matasan Najeriya masu zanga zanga a dandalin Eagle Square sun dakile ministan matasa, Ayodele Olawande daga yin magana yayin da suke zanga zanga a Abuja.
Ana cigaba da zanga-zanga a fadin Najeriya baki daya inda a halin yanzu ya rikide ya koma tashin hankali a manyan biranen Arewacin kasar a yau Alhamis.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana takaicin yadda marasa kishin jihar su ka shiga cikin masu gudanar da zanga-zanga wajen tayar da hankula da sata a jihar.
Gwamnatin jihar Yobe ta sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a yankunan Potiskum, Gashua da Nguru na jihar bayan da wasu ‘yan daba suka kwace zanga-zanga.
Rahotannin da muke samu sun tabbatar da cewa masu zanga-zanga a birnin Abuja sun durfafi yankin Asokoro inda ke dauke da manyan kasar Najeriya a yau Alhamis.
Rahotanni sun bayyana cewa masu zanga zanga sun farmaki ofishin hukumar KASTLEA da ke jihar Kaduna inda suka cinna masa wuta tare da wawushe dukiyar jama'a.
Rahotanni sun bayyana cewa zanga-zanga a Kano ta rikide zuwa fitina yayin da aka kashe wani matashi a Hoto, inda wani matashin kuma ke kwance bayan harbin bindiga.
Rundunar yan sanda a jihar Kaduna sun yi yunkurin bude kwanar Gwargaje da matasa masu zanga zanga suka toshe. Yan sanda sun fesa borkonon tsohuwa ga matasan.
Rundunar 'yan sandan jihar Borno ta sanar da sanya dokar hana fita ta awanni 24 a fadin jihar biyo bayan fashewar bam a wata kasuwa. Gwamna Zulum ya ba da umarnin.
Matsin tattalin arziki
Samu kari