Matsin tattalin arziki
Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar karfafi matasa masu zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a Najeriya, ya bukaci Bola Tinubu ya sauraresu.
Kungiyar gamayyar jam'iyyun siyasa a Najeriya, CUPP ta ce shugaba Bola Tinubu ya yi kuskure wajen hanyoyin da zai bi wajen shawo kan matasa masu zanga zanga.
Jama'a a jihar Jigawa sun fito zanga-zanga duk da haramcin fita na awanni 24 da gwamnatin jihar ta sanya. Jamai'an tsaro sun hana mutanen shiga yankin Zai.
Jagoran zanga zangar kungiyar Take it Back Movement, Damilare Adenola ya koka kan yadda yan sanda suka musu ruwan borkonon tsohuwa a birnin tarayya Abuja.
Wani bidiyo da ya yadu a shafukan sada zumunta ya nuna lokacin da Kiristoci ke ba Musulmai kariya a lokacin da suke yin sallar Juma'a ana tsaka da zanga-zanga.
Gwamnatin Kano ta ce ta sassauta dokar hana fita ta awanni 24 da ta sanya a fadin jihar a jiya Alhamis domin ba al'umma damar zuwa masallacin Juma'a.
Gwamnatin tarayya ta yi kira ga matasa masu jagorantar zanga zangar adawa da tsadar rayuwa kan su tattauna. Nyesom Wike ne ya yi kira ga matasan Najeriya.
Rundunar 'yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta yi magana kan harin da aka ce an kaiwa ofishinta na Nyanya a ranar Alhamis bayan da aka fara zanga-zanga.
Rundunar 'yan sanda ta yi shirin ko ta kwana yayin da masu zanga-zanga suka kashe jami'in dan sanda 1 da kuma lalata ofisoshin rundunar a sassan kasar.
Matsin tattalin arziki
Samu kari