Matsin tattalin arziki
Shugaba Bola Tinubu ya sake ba yan Najeriya tabbacin cewa yana daukar matakai masu muhimmanci domin rage tsadar rayuwa da ake ciki a kasa baki daya.
Matasan Najeriya sun fara zanga zangar adawa da tsadar rayuwa karo na biyu a watan Oktoba. Matasan sun fito kan tituna suna cewa suna jin yunwa a Abuja.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan halin kunci da ake ciki a Najeriya inda ya ce tabbas akwai kalubale amma komai zai daidaita nan ba da jimawa ba.
Babbar kotun jihar ta jero wurare huɗu kacal da ta amince masu zanga-zanga su taru a ranar 1 ga watan Oktoba, 2024, ya ba kwamishinan ƴan sanda umarni.
Wata ƙungitar matasa ta bukaci al'ummar jihar Kaduna su ci gaba da harkokinsu na yau da kullum, ka da su bari a yaudare su, su shiga zanga zangar yunwa.
Wani dan majalisar wakilai ya cire tsoro ya fadawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu gaskiya kan yadda tsare-tsaren gwamnatinsa suka jawo tsadar rayuwa a kasar.
Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya bayyana cewa nan ba da daɗewa ba duhu zai yaye, harske ya bayyana a Najeriya, ya roki mutane su ƙara hakuri.
A rahoton nan, Ministan kasafi da tsare-tsare, Atiku Bagudu ya kare manufoffin tattalin arzikin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu duk da koken yan Najeriya.
Kungiyoyin farafen hula sun fadi hanyar da Bola Tinubu zai bi wajen shawo kan matasa masu zanga zangar Oktoba. A ranar Talata matasa za su fara zanga zanga.
Matsin tattalin arziki
Samu kari