Hukumar EFCC
Babbar kotun tarayya ta fusta kan yadda Yahaya yake ci gaba da kin bayyana a gabanta. Mai shari’a Emeka Nwite ya yi fataki da bukatar hana EFCC kama Bello.
Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, ya bayyana a gaban kotu kan zargin badaƙalar N7.2bn. Sirika ya yi magana kan yiwuwar tafiya gidan kurkuku.
Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da belin tsohon ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika, ɗiyarsa, da wasu mutane biyu kan N100m kowanne.
Binciken gano gaskiya da aka gudanar kan hoton da ake yaɗawa cewa Yahaya Bello ya yi shigar ƴan Daudu ya gano cewa ba tsohon gwamnan bane a hoton.
Hukumar EFCC ta tabbatar da cewa za ta gurfanar da tsohon Ministan Buhari, Hadi Sirika a gaban kotu a gobe Alhamis 9 ga watan Mayu kan zargin wawushe N2.7bn.
Gamayyar kungiyoyin fararen hula karkashin kungiyar NCSO sun yi karar dan takarar gwamnan APC a zaben jihar Edo ga hukumar EFCC kan zargin ya ci zarafin Naira.
Jami'an hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) sun kai samame a kasuwar 'yan canji da ke Abuja. Sun cafke wasu 'yan kasuwa.
Tsawon shekaru da hukumar EFCC ta yi tana yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ta zargi tsofaffin gwamnoni sama da 30 kuma ta yi nasarar daure guda shida
Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa ta tsare wasu manyan jami'an hukumar sibil difence NSDCC a hedkwatar EFCC da ke Abuja.
Hukumar EFCC
Samu kari