Hukumar EFCC
A labarin nan, za a ji cewa tsohon Ministan Shari'a, Abubakar Malami SAN matarsa da yaronsu sun sake gurfana a gaban kotu a ci gaba da shari'a da EFCC.
A labarin nan, za a ji cewa hukumar EFCC ta samu nasarar shigar da karin takardu a shari'ar da ta ke yi da tsohon Shugaban NHIS, Farfesa Usman Yusuf.
EFCC ta gurfanar da daraktocin NRC guda 3 kan zargin wawure ₦2.04bn a Legas. An tsare Iloanusi a yari yayin da Njoku ya sami belin jinya a shari'ar.
Kungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC), ta shiga batun ci gaba da tsare tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai. Ta bukaci a kai shi kotu ko a sake shi.
Hukumar ICPC mai yaki da cin hanci da rashawa ta fito ta yi martani kan zargin cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya zubar da jini a hannunta.
A labarin nan, za a ji cewa hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta sanar da dalilan da suka hana ta gurfanar da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i gaban kotu.
EFCC ta bayyana dalilin jinkirin kai El-Rufai kotu. Ta ce tana son kammala bincike kafin gurfanar da shi yayin da yake tsare a hannun hukumar ICPC har yanzu.
Babban alkalin babbar kotun tarayya, Mai shari'a John Tsoho, ya mika kararrakin da hukumar EFCC ta shigar kan Abubukar Malami ga sabon alkalin da zai saurare su.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, na neman gwamnatin tarayya ta dauki alhakin lafiyar Nasir El-Rufai yayin tsare shi da ke janyo martani.
Hukumar EFCC
Samu kari