Kasar waje
Masana falaki sun tabbatar cewa jinjirin watan Shawwal zai kasance a sararin samaniya, amma saboda matsalolin yanayi da warwatsewar haske, ba zai yiwu a gan shi ba.
Gwamnatin Birtaniya ta fitar da jerin kadarorin da wasu 'yan Najeriya 60 suka mutu suka bari, kuma har yanzu babu wani magajinsu da ya je ya karɓe su.
Shugaban Sudan ta Kudu, Salva Kiir, ya kama mataimakinsa, Riek Machar. Kasashen waje na rufe ofisoshinsu yayin da rikicin basasa ke shirin barkewa a kasar.
Sojojin Najeriya 171 sun samu horo mai inganci a cibiyar MLAILPKC domin gudanar da aikin wanzar da zaman lafiya a Sudan. An bukace su da su kiyaye dokokin UNISFA.
Rahotanni sun ce wasu mutane da ba a san ko su waye ba sun kwace wata mota dauke da kayan tallafin abinci ta hukumar WFP a garin Gubio da ke jihar Borno.
Dan daudu mai shigar mata da ya tsere daga Najeriya ya ce ya bar kasar har abada. Bobrisky ya ce a Najeriya har Sanatoci da ministoci na magana a kansa.
Malamin addinin Musulunci na duniya, Sheikh Abu Ishaq Al-Huwaini ya rasu a kasar Masar. Malamin ya shafe shekaru 69 a duniya kuma ya kasance malamin Hadisi.
Daraktan kamfanin man fetur a Nijar ya ce an shiga matsalar man fetur bayan yanke alaka da China, sauke farashi da yawan bukatar fetur a fadin kasar.
Rahoto ya bayyana cewa, kasar Saudiyya bata kai Najeriya ba wajen kashe kudi idan ana hako mai. An bayyana adadin kudaden da Najeriya ke kashewa da na Saudiya.
Kasar waje
Samu kari