Kasar waje
Jagoran adawa na Kamaru, Issa Tchiroma Bakary, ya zargi gwamnati da kulla shirin tsoratarwa da garkuwa da iyalansa bayan zaben shugaban ƙasa da aka yi.
Gwamnatin shugaba Paul Biya na Kamaru ta ce za ta gurfanar da jagoran 'ya adawar kasar da ya ce ya lashe zaben shugaban kas, Issa Tchiroma Bakary kan tarzoma.
Isra'ila ta kai sababbin hare hare masu muni Gaza bayan sulhu da Amurka ta jagoranta a Oktoba. Sojojin Isra'ila sun kashe mutum sama da 100 a Falasdinu.
Ministan makamashin Najeriya, Bayo Adelabu ya ce Najeriya ta fara fitar da kayan sola da ta kare zuwa kasuwannin Afrika ta Yamma. Ya ce an fara fitar da su Ghana.
Rundunar sojojin ruwa ta kasar Amurka ta tabbatar da hatsarin jiragenta biyu a tekun kudancin China, ta ce babu wanda ya rasa rayuwarsa a hadurran biyu.
Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria a jihar Kaduna ta karyata wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta da ya zarge ta da kera makamin nukiliya.
An sanar da rasuwar matar tsohon shugaban kasar Ghana, Nana Konadu Rawlings wacce ta riga mu gidan gaskiya tana da shekaru 79 a duniya bayan fama da jinya.
Wata kotu a Ingila ta daure dan Najeriya na watanni 16 a gida yari kan amfani da sunan mace wajen yin aiki a wani asibiti, ta kuma ci tarar mutumin makudan kudi
Gwamnatin Kamaru ta sanar da cewa za ta gurfanar da matasa akalla 20 da aka kama a kotun soja kan zanga zangar bayan zaben shugaban kasa saboda tayar da tarzoma.
Kasar waje
Samu kari