Jam'iyyar APC
A labarin nan, za a ji cewa tsohon Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya karbi Baƙuncin Mai magana da yawun Gwamna Abba Kabir Yusuf a gidansa da ke Abuja.
Sanata Hanga ya umarci tsofaffin shugabannin NNPP su dawo da motocin da ya ba su bayan sauya sheka zuwa APC a Kano; AA Zaura ya yi alkawarin ba su wasu sababbi.
A labarin nan, za a ji cewa Ministan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa mai ritaya ya sanar da shirin da ya ke na tsunduma harkokin siyasa gabanin 2027.
Kwamishiniyar harkokin mata da yara a Kano, Hajiya Amina Sani (Amina HOD), ta fice daga NNPP zuwa APC, lamarin da ya tayar da kura a siyasar jihar.
Abdulmajid Dan Bilki Kwamanda ya bayyana cewa ficewar Abba Kabir zuwa APC babban butulci ne ga Rabiu Kwankwaso, yana mai cewa gwamnan zai fadi a zaben 2027.
Kwamishinan yada labarai a Kano ya ce rikicin cikin gida ya lalata NNPP, yana mai cewa canjin tambari daga kwandon kayan marmari zuwa littafi ne ya haddasa matsala.
Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya bayyana sauya sheƙar Gwamna Agbu Kefas zuwa APC a matsayin abin alfahari da ya taba zuciyarsa matuƙa.
Jam'iyyar NNPP ta musanta cewa Sanata Rabiu Kwankwaso ya tattauna batun komawa APC da Tinubu; ta bayyana rahoton a matsayin ƙarya da nufin ɓata masa suna.
Dan majalisar wakilai, Hon. Alhassan Ado Doguwa ya bayyana cewa sun hade da Gwamna Abba Kabir Yisuf kuma za su yi aiki tare domin nasarar jam'iyyar a zabuka na gaba.
Jam'iyyar APC
Samu kari