Dan Wasan Kwallon Kafa
Mun kawo maku jerin ‘Yan wasa 5 da su ka gama rayuwar kwallo ba tare da karban jan kati ba. Akwai irin su Ryan Giggs da Van Der Sar da Del Piero da kuma irin su Raul Gonzales da yayi kwallo a Birnin Madrid tun yana yaro.
Bisa dukkan alamu ana ganin Neymar zai iya komawa bugawa manyan ‘yan adawan Barcelona watau tsohon Kulon din ya baro na Real Madrid. Mun kawo abubuwan da za su iya sa ‘Dan wasa Neymar ya tattara ya bar PSG a karshen bana.
Idan ka ji labarin ‘Dan kwallon da ya fi kowa dukiya za ka yi mamaki. Yanzu haka Faiq Bolkiah mai shekaru 19 a Duniya ya sha gaban irin su Lionel Messi da Cristiano Ronaldo na Barcelona da Kungiyar Real Madrid.
Za ku ji cewa Dan wasan gaban Brazil Neymar Jr. ya ji dama bai bar Kungiyar sa ta Barcelona zuwa PSG ba a karshen kakar da ta wuce bayan ya fara gamuwa da cikas
A karshen makon jiya ne mu ka ji wani Boka ya bayyana abin da ya ja wa Cristiano Ronaldo tasgaro. Yace Dan wasan bai bar alaka mai kyau tsakanin sa da uban sa.
HAYau za ayi ta ta kare tsakanin Real Madrid da Barcelona. A karon farko dai Real Madrid tayi nasara da ci 3-1. Wanda yayi nasara zai lashe Gasar Super Copa.
Barcelona na neman wanda zai maye gurbin tsohon Dan wasan ta Neymar da ya tashi. Daga ciki akwai iIrin su Coutinho, Dembele, da Mpape har da su Griezman.
Muna samun labari daga Kasar Sifen cewa Kungiyar Real Madrid ta shiga yarjejeniya da Monaco domin sayen Dan wasa Mbappe wanda zai ci kusan Euro Miliyan 180.
Ana zargi Dan wasan Real Madrid Ronaldo bai biya wasu kudin haraji ba. Haka kuma wasu 'Yan wasan irin Di maria ta tabbata cewa su masu laifi ne a gaban Hukuma.
Dan Wasan Kwallon Kafa
Samu kari